MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 7

_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(7)

FA’IDARTA GA MAI BAYARWA:
TARE DA
FA’IDARTA GA MASU KARBARTA
:
Zakkar tana da amfani ga wanda ya fitar da ita ta fuskoki kamar haka :-

1-Tana koyawa mai fitar da ita kyauta, 
ta fitar masa da rowa daga cikin zuciyarsa.
" Watau zai koyi yin kyauta ya bar rowa. 
Rowa mummunar dabi’a ce wadda ke cutar da mai yin ta.

 Allah (SWT) Ya ce:
 (ومن يوق شح نفسه فأولئك هم المفلحون)

Ma’ana: “Duk wanda aka kare shi daga rowar kansa, 
to wadannan sune masu rabauta”.

 Haka kuma Manzon Allah (SAW) ya ce:

"إياكم والشح فإنه أهلك من كان قبلكم الشح".

Ma’ana: “Ku kiyayi rowa. 
HaKiKa wadanda suke gabaninku sun halaka ne ta hanyar rowa”
 (Abu Dauda ne ya rawaito shi).

2.Tana fitar da mai bayar da ita daga Kangin bauta wa dukiya, izuwa mallakarta. 
Domin duk wanda zai tara dukiya amma ba zai iya bayar da ita ba, 
to bauta mata yake yi. 
Ita ta mallake shi, 
ba shi ya mallake ta ba. 

Manzon Allah (SAW) ya yi addu’a mummuna ga wanda abin duniya ya tsokane masa ido, kamar haka:-

"تعس عبد الدينار، وعبد الدرهم، وعبد الخميصة، تعس وانتكس. وإذا شيك فلا انتقش".

Watau: “Bawan dinare ya halaka, 
da bawan dirhami, 
da bawan riga 
(ko mayafi).  
Allah Ya tuntsurar da shi ta fuska. 
Allah ya tuntsurar 
da shi ta ka.  
Kai idan ma ya taka Kaya, kada Allah Ya sa ta fita". 
(Bukhari ne ya rawaito.)

3. Tana koya wa mai bayar da ita godiyar Allah a aikace. Domin idan bawa ya sarrafa ni’imar da Allah Ya yi masa ta umarninSa to shi ne ya yi godiya a aikace.

 Idan har mawadaci zai dubi halin da matalauci ke ciki amma ya Ki taimaka masa, 
to babu shakka bai gode wa Allah ba.

4. Yakan sami Karuwar dukiyarsa. Amma fa ya kamata mu sani cewa Karuwar dukiya ba ta tsaya ga yawanta kawai ba. A’a! idan ta yi danKo ta zarce har ‘ya’ya da jikoki ai ita ce babbar albarka. Balle kuma idan alherinta yana tafiya lahira.  

Ka da kuma mu manta cewar, Allah Ya yi rantsuwa da cewar, idan muka gode maSa zai Kara mana:
(ولإن شكرتم لأزيدنكم) 
Ma’ana: “Idan kuka gode, to lallai Zan Kara muku”.

5. Yakan sami soyayya da Kauna daga mutane. 
Domin duk mai taimakawa mutane yana tare da samun Kaunarsu.

FA’IDA GA MASU KARBARTA:

 Zakka tana da fa’idoji masu yawa ta bangaren masu karbarta. Daga ciki akwai:

1. Wanda ya sami Zakka, 
yadda ya kamata a bayar da ita, za ta fitar da shi daga talauci ko bauta ko bashi.

2. Tana tsarkake zuciyar matalauta daga yin hassada ga mawadata, 
da jin Kiyayya da Kyashi a gare su.

3. Tana Kara mutunci da kuzari ga wanda ya karbe ta. 
Domin tsananin talauci yakan kawar da wadannan suffofi daga mutane. Musamman ma a wannan zamani da muke ciki.

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Post a Comment (0)