NA GANSHI A ALJANNA


*🌺NA GANSHI YA SHIGA ALJANNA🌺*


بسم الله الرحمن الرحيم.


🌺Wani mutum daga mutanen *sham* yazo sai yace ku nunamin *Safwan bin salim* domin na ganshi *ya shiga aljannah* Sai nace da wanne aiki? (ya shiga aljannah) sai yace saboda da wata Riga daya tufatar da ita ga wani mutum, sai wasu mutane sukace mun tambayi safwan game da labarin wannan Riga sai yace:👇

_*🌺Watara na fita daga masallaci da dare ana sanyi sai kawai naga wani mutum tsirara (Babu cikakkun kaya ajikinsa) Sai na cire rigata na saka masa*_

صفوة الصفوة٢/١٥٤


                              *🌺DARASI🌺*


🌺Yanzu da zamu koma da kunanmu mu duba kayanmu da zamu samu kayan da bama bukatarsu sam a wardrobe dinmu, to mai yasa baxamu fito dasu mu bawa mabukata ba!?

🌺Allah yayi maka ni'ima kema yayi miki ni'ima ya rufa maka/ki asiri har ka samu ka dinka kayan sallah, wani ma idan yana da iyali ma ya dinka musu tun kafin zuwan azumin nan, to amma shin wanne tanadi kayiwa talakawa da marayun da suke kewaye dakai wajen ganin ka faranta musu rai? ka nemi lada da yarda da kuma Neman aljannah kamar yadda wannan bawan Allah yayi!??


🌺Ya fifita bukatar dan uwansa musulmi akansa ya cire rigar dake jikinsa ya tufatar da Dan uwansa domin tausaya masa sakamakon haka yayi masa tagomashi da Shiga Alannah. Yan uwa a wannan lokacin da aka shiga kunci da talauci shine yafi dacewa da mu taimaki yan uwanmu, wallahi wata set din kayanta sunfi kala 50, wata ma zaki samu tana da 100, haka bangaren mazan, to amma kuma a hakan kullum so muke mu kuma yin sababbi, amma inaga talaka inaga maraya? 

🌺Hadisi ya tabbata ruwayar bukari da Muslim daga Abdullahi bin umar (R.D) Annab i(S.A.W) yace: _*Duk wanda ya yayewa musulmi bakin ciki daga cikin bakin cikin duniya Allah zai yaye masa bakin ciki daga cikin bakin cikin duniya da lahira*._

🌺Yan uwa wannan itace dama a garemu da zamuyi taimakon da zamu nemi aljanna, Riga daya ta bashi aljanna to inaga ke ina ga kai da zaka bada Set 5 ko 1 ko 2 ko sama da haka? 

🌺Allah ya bamu ikon taimakawa da ikhlasi ya bamu ikon Shiga Aljannarsa.

 
✍Rubutawa: *Ummul Banaat*
فردوس ثانى علي


https://www.facebook.com/sawtulhikmah

https://t.me/sawtul_hikmah

_*🎙ZAUREN SAWTUL HIKMAH 🎙 (da'awar sunnah a social Media's) 🌎*_

*• Ga masu buqatar shiga Zauren Sawtul hikmah sai a turo da cikakkiyar sallama tare da Cikakken suna da Address ta wadannan Numbobi kamar haka:- +2348060027244 ko +2348039375380 a whatsapp.*
Post a Comment (0)