IYAYENA MATA KU KARE MUTUNCIN KAN KU

*👩 IYAYENA MATA KU KARE MUTUNCINKAN KU!!👩*

⚫ Yan Uwana Mata, iyayena da yayyena, da 'kanne na, ina muku sallama irinta addinin Musulunci, sallama irinta yan aljannah *Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu* 👋

🙏 Bayan haka ina sake gaishe ku. 

⚫ A kwanakin baya da jimawa mun tabayin *TUNATARWA* wacce ni da kaina na rubutata, toh amma naga kamar an fara mantawa da karatun, wanda gaskiya da farko an fara aiki da karatun, toh amma yanxu naga alamar an manta, Duniya ta kuma yi mana dadi .

⚫ *TUNATARWAR* nayi ta ne akan *DUBA HOTONKA/KI NA D.P* wato tana magana ne akan Masu saka hotunan su barkatai a d.p koh status babu kulawa da irin wanda zasu saka, koh wanda ya dace su saka ka.

⚫ Saboda lalacewar mu kullin yawa take kuma yi, yanxu abin ya kuma baci zaku samu cewa abin ya bar gurin *'yan mata* kawai, ya zamana har da *Matan Aure* 

Ni wallahi kuna bani mamaki iyayena mata. 🤔

⁉ Shin ba kya tsoron wani ya dauki hutun naki ne yayi saving a wayarsa ya tafi yana yadaki??!

⚫ Munyi wa'azi, kuma mun sha gaya muku cewa WALLAHI HARAMUN NE! Mace Budurwa, koh matar aure, ta saka hotun ta a d.p ta yadda kowa zai gani!

⚫ Baki da hujjar kare kanki a gurin *ALLAH (S.W.A)* Baki kuma da abinda zaki gayamasa na kare kanki!!

⚫ Tunda munce muku haramun ne, Mun kuma ce daku zubar da mutuncin kan ku ne da kimarku da Hulakantar da kanku da tallatar da kanku da mayar da kanku a banza garabasa. Ta yadda kowa zaiyi abinda ya ga dama daku, ta yarda kowa zai tayaku yadda yake so, kun mayar da kanku arha. Amma Ku kuma kunce A'a sai kunyi, ai hakan duk ba komai bane, toh shikenan. Dama ance *Duk wanda baiyi sharar Masallaci ba toh tabbas zaiyi ta coci!!* Don idan kika yi ta kasuwa toh abin da sauqi.

⚫ ⁉ Wai ni ga tambaya zuwa gare ku *shin mai kuke ji idan kun sa huton ku a d.p, koh status, musamman ma zuwa ga shafin instagram koh facebook??* Ni dai na san dayan ukun nan ne:

1- Ko dai kina so ace ke kyakkyawace! Koh ace you sexy?! Da makamantansu

2- Koh kuma kina neman samari ne?

3- Koh kuma dai kina sawa don ace wacce tafi kowa kyau, kuma tafi kowa followers!

⚫ Koh don ki nunawa mutane cewa ke yar kauyece. Don in ba 'yar kauye ba toh babu wacce zata dinga daukan hoto a ko ina ta na sakawa a d.p dinta koh status. 

⚫ Yanxu saboda lalaci har wani app akayi wai shi *snap chart* shi wannan app din duk abinda kikeyi a lokacin zaki iya video koh hoto ki saka, kuma duk wanda yake dake xai ga abinda kika sa. 

⚫ sai kaga Yarinya ta dauki hoto a bandaki, koh a kitchen, koh a makaranta, koh tana kwance, koh tana cin abinci da makamantansu. Saboda shirme da hauka!!

⚫Duk wadannan abubuwa wallahi ba da ka nake fada ba, don kuwa duk ina da account dinsu, wasu ma na bude da boyayyen suna, ba don komai ba sai don na ganewa ido na barnar da akeyi!

⚫ Shiyasa sai kaga Yarinyar ka ta lalace kai kuma ka rasa yadda akayi ta lalace din! Gashi dai bata zuwa ko ina, amma ka barta da abinda yake saurin canzawa yaro tunani wato *WAYA/ HANDSET 📱*

Kaga Yarinya tana rike wayar #200000 ko fiye da haka, ka rasa ta yadda akayi ta samu kudin.

⚫ Kuma dah kafin yanxu, iya manyan wayoyi ne suke hawa internet, toh amma yanxu wannan "baby nokia" itama sai an mata wani dan app na chart, yanxu zaku ga sukan zo da wani chart mai suna *palm chart* shima dai gashi nan shigen sauran ne.

⚫ Toh Wallahi yakamata iyaye ku tashi tsaye akan 'ya'yanku, yanxu pha yarinya bata zama Mazinaciyya ta hanyar ta fita ta hadu da samari. Yarinya ta kan zama Mazinaciyya ta na zaune a gida matuqar tana da waya!

Don kuwa akwai *social media's 📡* groups da suke da kungiyoyi na yan "madigo, koh Mazinata" yarinya shiga kawai zatayi tayi register dasu, to daga nan shikenan ta zama yar kungiya, kuma duk wani video koh abun lalata da iskanci za'a turo mata. Har samari akan yi musu a irin wadannan guraren. 

⚫ kai kana can kana neman na tuwo, ita kuma ta nan ta zama 'yar kungiya har kudi da kati ake turo mata! Sai anyi magana sai kace ai wacce akwai tarbiyya.

⚫ Kuma wallahi babban abin haushi da takaici shine harda *Matan Aure!!* Ire iren wadannan guraren harda nasu personal, wani gurin ma sai ance tayi bayani akan mijinta, yaya take saduwa dashi, ya take mu'amala dashi da sauransu. Kuma wallahi saboda rashin mutunci haka zatayi wadannan bayanan don a saka ta a kungiyar.

⚫ ire iren wadannan fituntunun sunanan da yawa babu adadi. Kullin sababbi ne suke kuma fitowa.

⚫ Saboda haka yanxu idan ALLAH ya baka 'ya mace toh wallahi baka ga ta zama ba, dole ka tashi tsaye akanta, ka saka ido, kuma har babar tata itama ka saka mata ido. Don baka san mai zeje ya daho ba.

⚫ Gashi dai kullin malaman mu karantarwar sukeyi amma abin kamar bayi ake ba, yanxun nan zaka yiwa Yarinya wa'azi tayi kamar ta jika amma wallahi wata har kuka zata fashe dashi tana cewa ta tuba, amma zuwa anjima zaka sake ganinta a gurin shedanci. Sam na rasa mai yake damun mu wallahi!!

⚫ Ga *SHIGAR BANZA* da ta yiwa Yara da 'yan matan yanxu yawa, harda masu auren babu wanda zaka dauke.

⚫ Wannan lalatar yanxu tafi yawa a makarantun mu na *Jami'a* kaga yarinya tayi shiga kamar ba yar musulma ba, wallahi yadda 'ya'ya mata musulmai suke shigar banza yanxu sunfi 'ya'yan kafiran ma! Don wallahi wata inda kasan 'yar gidan Pastor haka take!

⚫ Ga wani Katon Tabarau (glass) da suke sakawa, wai shima wannan wanka ne, kaga yarinya ta saka jambaki dukka lebanta kamar wata 'yar maye! 

⚫ Yanxu a haka muke so mu mutu muje mu sami Rahmar Ubangijin mu?? Koh a haka muke so a dinga yi mana ruwan sama? Koh kuma a haka muke so dala da kayan abinci su sakko??!

⚫ WALLAHI baza mu taba samun Rahmar Allah ba sai mun gyara. kuma gyaran ya fara tun da ga kanmu ne ba wai tsayawa zamuyi ba muce sai wani yayi sannan zamuyi ba dole mune zamu gyara.

⚫ Idan koh bamu gyara ba toh haka shima ALLAH ba zai fasa sauqar mana da azabarsa ba! 😭

ZAN TSAYA ANAN SAI A CIGABAN ZAMUJI MATSALOLIN DA BALA'UN DAKE TATTARE A WANNAN MUSIBA IN SHAA ALLAHU.

✍ Dan Uwanku a Musulunci Da Sunnah:- *Abdullah A Abdullah Assalafeey*

13/11/2017

*· Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallama tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)