SUNNONI DA LADUBBA GUDA 17 NA RANAR IDI


SUNNONI DA LADUBBA GUDA 17 NA RANAR IDI

*1-Yin ado da kwalliya dan ranar Idi*

Saboda Hadisn Umar bin kaddhaba R.A.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 948.

*2-Yin wankan ranar Idi kafin tafiya sallar idi*

Ibn Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wankan idi.
@ﻣﻮﻃﺄ ﻣﺎﻟﻚ، 384.

Sa'id bn Musayyib Allah yayi masa Rahama yana cewa:
*"Manyan sunnonin ranar Idi guda ukku ne tafiya masallacin idi a kasa da cin abinci kafin afita a idin karamar sallah da kamewa daga cin komai sai an dawo a babbar Sallah da yin wankan idi"*
@ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ‏( 3/104 ‏) ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ.

*3-Yin sallar idi kafin Huduba*

Manzon Allah s.a.w da Abubakar da Umar sun kasance suna yin Sallar idi kafin Huduba.
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ - ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺼﻼﺓ-ﺗﻔﺮﻳﻊ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺑﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ :972 ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻰ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻰ ﺩﺍﻭﺩ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ 1134 0

*4-Haramunne yin Azumi a ranar Idi guda biyu,idan azumi da idin Layya*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Babu azumi a ranakun idi guda biyu,idin azumi da idin Layya)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ،1197

*5-Cin abinci ko wani abu kafin tafi sallar idin azumi,kuma anfi so aci dabino kuma aci mara sabanin Idan layya ana kamewa ba'acin komai sai an dawo daga Idi*

Manzon Allah s.a.w ya kasance baya tafi sallar idin azumi har sai yaci Dabino kuma yana cin dabinon ne mara.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 953.

*6-Yin sallar Idi a musalla shine sunnah wato a bayan gari a wani fili ba masallaci ba*

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana fita musallane don yin sallar idi.
@ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 510.

Ibn Umar R.A yana cewa:
*"Manzon Allah s.a.w yana fitane da wuri zuwa musalla dan yin sallar idi...."*
@ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ، 1294

*7-Sunnane a fitar da mata da yara zuwa sallar idi,amma matan suyi shiga ta musulinci kuma kada su sanya turaren da kamshensa yake tashi*
@ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 511.

Sayyadina Abubakar R.A yana cewa:
*"Hakkine akan kowace budurwa da macen aure fita zuwa sallar idi"*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ .

*8-Tafiya masallacin idi kasa idan da ikon hakan*

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana tafiya masallacin idi akasa kuma ya dawo akasa.
@ﺣﺴﻦ / ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 1078 ‏( 1311 )

Aliyu bn Abi Dhalib R.A yana cewa:
*"Yana cikin Sunnah tafiya sallar idi a kasa kuma aci wani abu kafin a fita idi"*.
@ﺣﺴﻦ /ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 530

*9-Chanza hanyar dawowa ko hanyar zuwa masallacin idi*

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana chanza haryar dawowa daga masallacin idi.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 986.

Ibn Umar R.A yana cewa:
*"Na koya daga Manzon Allah s.a.w chanza har dawowa daga masallacin idi*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 254.

*10-Yin kabarbari na ranar Idi*

*_Ana fara kabbarar ne daga Faduwar Ranar karhen ta Ramadhana idan an ga watan Shawwal za'a fara yin kabbarori har zuwa fitowar LIMAN dan yin sallar IDI_*

Imam Sun'ãni yana cewa:
*"Yin kabbar tun daren idi har zuwa fara sallar idi yin hakan sunnane abisa haduwa mafi yawan malamai saboda farrasa fadin Allah Madaukakin sarki*-
*(ﻭَﻟِﺘُﻜَﺒِّﺮُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻫَﺪَﺍﻛُﻢْ ﻭَﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺸْﻜُﺮُﻭﻥَ )*
@ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 185
@ ﺍﻟﺼﻨﻌﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺳﺒﻞ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﺍﻟﺠﺰﺀ ﺍﻟﺜﺎﻧﻲ : 100-101 .

*11-Sigogin Kabbarorin ranar Idi*
Daga Cikin sigogin da aka samo daga Sahabbai sun hada da;-

Siga ta farko;-
*ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺃﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ*
@ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ.ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ ‏( 3/125 ‏)ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ.

Siga ta biyu;-
* ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ*

Siga ta Ukku;-
* ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻭﺃﺟﻞ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻫﺪﺍﻧﺎ .
@ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﺒﻴﻬﻘﻲ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ . ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ
‏( 3/125 ‏)ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ

*12-Sanya Turare dan zuwa sallar idi*

Abdillahi dan Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wanka ya sanya turare.
@ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ - ﺑﺎﺏ ﻣﺎ ﺭﻭﻱ ﻓﻲ ﺍﻻﻏﺘﺴﺎﻝ ﻟﻠﻔﻄﺮ ﺣﺪﻳﺚ 015

*13-Ba'a sallar nafila kafin sallar idi ko bayanta,kuma ba'a kiran sallah ko iqama*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ - ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ :1517
@ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ - ﺑﺎﺏ ﻣﺎﺭﻭﻱ ﺃﻧﻪ ﻻ ﺻﻼﺓ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻗﺒﻞ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﻻﺑﻌﺪﻫﺎ ﺣﺪﻳﺚ 0143

*14-Yin gaisuwar sallah da fatan Alkhairi da fatan Allah ya maimata mana*

An samu daga aiyukan maganata suna yiwa junansu barka da sallah da fatan alkhairi,daga cikin abinda suke fada akwai;-
*ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻚ*

*15-Yin wasa na al'ada wanda babu sabon Allah acikinsa dan nuna farincin ranar Sallah,sannan mata zasu yi nasu wake da buda kayan kidansu na al'ada wanda babu sabon Allah*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ - ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ - ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ - ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺤﺮﺍﺏ ﻭﺍﻟﺪﺭﻕ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ - ﺣﺪﻳﺚ :921 ، ﻭﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ - ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ - ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺮﺧﺼﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻌﺐ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻣﻌﺼﻴﺔ ﻓﻴﻪ ﻓﻲ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ - ﺣﺪﻳﺚ 01527:

*16-Cin wani abu daga cikin abinda ka yanka na layya bayan dawowa daga sallar Idi*

Manzon Allah SAW ya kasance baya cin abinci a idin babbar sallah har sai ya dawo daga Masallaci sannan yana fara cine daga wani sashe daga abinda ya yanka na layyarsa.
@ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ / .144

*17-Girmama ranar Idin layya akan sauran ranaku domin ranace mai girma awajan Allah*

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Mafi girman ranaku a wajan Allah sune; Ranar Layya da ranar washe garin Layya)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ 

  Allah ne mafi sani

*Ina yiwa dukkan musulmai barka da sallah da fatan alkhair,Allah ya maimata mana*

* ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻚ*
Post a Comment (0)