*HUKUNCIN BAWA MATAR AURE ZAKKAR FIDDA KAI*
*Tambaya :*
Assalamu Alaiykum, Malam Shin ya halasta in baiwa matar aure zakkatil- fitr?
*Amsa :*
Wa alaikum assalam To dan'uwa malamai suna cewa ya halatta a baiwa matar aure zakkar fidda kai, mutukar tana cikin bukata, saidai wasu malaman suna cewa mutukar tana da miji wanda zai wadatar da ita, to ba za'a bata ba, domin yana daga cikin hikimomin zakkar fidda-kai wadatar da mutane a wannan ranar, daga barin roko.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
22/3/2014