TAKAITATTUN FATAWOWI MASU MUHIMMANCIN DA SUKA KEBANCI 'YAN UWA MATA
*FITOWA TA 1*
*TAMBAYA*
Akan samu wasu daga cikin mata ana bin su azumin Ramadan ba su rama ba har wani Ramadan din ya riske su. Ina hukuncin wannan?
*AMSA*
Abun da yake wajibi akansu shi ne su tuba zuwa ga Allah su daina irin haka, domin ba ya halatta ga wanda ake bin shi azumin Ramadan ya jinkirta shi zuwa wani Ramadan din ba tare da uzuri ba. Domin Nana A'isha, Radhiyallahu anhaa ta ce: *_"Ya kan kasance ana bi na azumin watan Ramadan, ba na iya rama shi sai a watan Sha'aban"_*.
Wannan yana nuni akan ba ya yiwuwa mutum ya jinkirta ramuwan azumin watan Ramadan har zuwa wani Ramadan din, don haka ya zama wajibi a gare ta, ta tuba kuma ta rama azumin da ake bin ta bayan ta kammala azumin Ramadan na biyu da ya riske ta.
Mu hadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta'ala.
Wanda ya amsa: *_Sheikh Muhammad Salih al-Uthaimeen, Rahimahullah_*
Tattarawa:
*_Umar Shehu Zaria_*
A duba:
فتاوى المرأة المسلمة يجيب عليها أصحاب الفضيلة العلماء.
Shafi na 338
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248
