TAMBAYA TA 122

TAMBAYA 1,720
Assalamualaikum malam watace suka samu masala da mijinta akan taka wando mijin Yana taka wando shine tayi mai magana akan ya daina takawando baida kyau, sai yace idan Bata kawo masa hadisin da aka hana taka wando ba abakin aurenta,to shine take cewa taji ance idan miji yacewa mace abakin auren ta Yana mazaunin saki uku, tana neman mafita,don sanin ta bai kai ta kawo mishi hadisi ko aya ba na gode
AMSA
Ya kamata mu sani cewa hukuncin tufafi haramcinsa wuce idon sawu ne ba takawa ba, shi takawan abin ya ma ƙara muni ne. dalilin wannan maganan shine hadisin da imam bukhari ya rawaito hadisi na 5787 da imam Ahmad vol 2 pg 461 daga Abu huraira (RA) annabi (saw) yace ((dukkan abinda yayi ƙasa da idon sawu na izari (zani) to yana wuta)) sannan akwai kwatankwacin wannna riwayar ma a cikin sunanin Nisa hadisi na 5331 da ibn majah hadisi na 3573. To amma mutum zai iya cewa wannan hadisin ai annabi izari yace wato (zani), to akwai hadisin dake cikin Ɗabarani (kabir) dagan Abdullahi ibn Abbas annabi (saw) yace ((dukkan WANI ABU DA YA WUCE IDON SAWU na izari to yana wuta )) sannan akwai riwayar Muslim wanda annabi yace ((mutane uku Allah bazai musu magana ba sannan bazai kallesu ranar qiyama ba kuma suna da azaba mai raɗaɗi: mai jan mayafinsa, da mai gori bayan yayi kyauta da mai siyar da kayansa da rantsuwar ƙarya)) kaga nan annabi ya haɗe komai, kuma annabi yakanyi magana ne a zamaninsa da abin da suke amfani dashi kai kuma sai kayi ƙiyasinsa a abinda kake amfani dashi yau kaga mu madadin izari da suke sawa shine mu mukesa wando, sannan malamai sun tabbatar da hamaramcin yana kan wanda ya bari wanda ya wuce ne haka amma in har ya zama don girman kai to haramcin ya ƙaru saboda annabi a sake yayi magana.
Wannan bayanin na cikin fathul baari sharhin sahihul bukhari na ibn hajar vol 10 pg 376 da kuma fatawa ibn baaz. Wallahu aalam
Amsawa:Mal Adam Daiyabu

Post a Comment (0)