TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 25


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//25📿*

*GINSHIQI NA 23*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

ME ZAI BIYO BAYA?

Yana da kyau a riqa yin lissafi, wannan abin da nake son fadi ko aikatawa me zai biyo baya? Mu sani fa Allah SW bai sanya lamuran Shari'a da hukunce-hukunce ba sai don mu tabbatar da kyawawan abubuwan da ake buqata, mu yi nesa da munana, don haka ya zama dole a wurin dalibin ilimi ko wani malami mai wa'azi ya sanya maganin qare-gau, shin in ya fadi wannan maganar ko ya yi wannan aikin me zai faru a qarshe? Shin akwai matsala ko babu?

In ya kasance yana da tabbacin akwai nasara, ko yana tsammanin akwai din to ya yi qoqarin aikatawa, in kuwa ya gano cewa tabbas a gaba akwai matsala, ko ya yi tsammanin za a iya samunta to ya haqura kawai, wasu abubuwan ba jinsu ne magani ba gyaran da zai biyo baya ake buqata, Allah SW ya yi gargadi a irin sakin harshennan ya ce ((Kar ku zagi wadanda suke bautar wani da bai kai Allah ba, don kar su juyo suna zagin Allan ba tare da ilimi ba adawa kawai)) Al'An'am 108.

Ibn Taimiya yana cewa "Gamammiyar qa'ida game da fito na fito da abubuwan da suke gyara da wadanda suke barna, da abubuwa masu kyau da munana ko su hade gaba-daya, anan ya zama dole a fitar da guda daya, idan gyara da barna suka yi fito na fito to dole a rabe, idan abinda ake son a cimmawa abu ne mai kyau da tunkude barna to sai a duba abinda zai haifar, in ya kasance barnar ta fi gyaran yawa to ba a yi umurni da aikata shi ba, tabbas haramun ne don barnar dake ciki ta fi gyaran yawa".

Ya yi wani babi na masamman ya ce "Idan aka sami fito na fiton kyawawan abubuwa da munana" yake cewa a ciki "Ana iya juriyar mummunan abu a dauke shi a wuri biyu: In ya kasance akwai abinda ya fi shi muni kuma ba za a iya tunkude mafi munin ba sai da shi, ko akwai abinda samunsa ya fi rashinsa, amma ba za a iya samu ba sai da wannan mummunan, haka kyakkyawan abu ana iya barinsa a wasu dalilai guda biyu: Idan ya kasance a dalilinsa za a iya rasa wanda ya fishi kyau, ko kuma za a gamu da wani mummuna da zai ci gaba da cutarwa sama da abinda ake samu na kyakkyawan, wannan yana da alaqa ne da ma'aunai a cikin addini.

Har dai zuwa inda ya ce "Idan aka sami ababan kuskure guda biyu amma ba zai yuwu a hana wanda ya fi girma ba sai da aikata mai sauqin, a irin wanan yanayi gaskiya hakan ba laifi ba ne (Al-Fatawa 20/53-61), a wani hadisi na Annabi SAW da aka karbo daga A'isha RA take cewa: Manzo Allah SAW ya ce "A'ishah, ba don mutanenki sun yi rayuwar shirka [Kafin muslunci] ba da na rushe Qa'aba har qasa, sannan na saka mata qofar gabas da ta yamma, na qara ma ta zira'i shida, Quraishawa sun gaza ne a lokacin ginin Qa'abar (Buhari 1509)" ga abinda Annabi SAW yake son ya yi, ya san yadda ginin yake a baya, qila dai akwai abinda ya sami Quraishawa ne ya hana su iya kai shi asalinsa, sai ya so shi ya kai din, amma yadda jama'a za su yi daga baya, sai ya kalli wannan ya haqura.

Buhari ya rawaito cewa Ibn Abbas ya na fadi cewa wani labari ya riski Umar a Mina a qarshen hajjinsa da ya yi, ya ji wani na cewa "Da Umar ya rasu da na yi wa wane mubaya'a, ai ko mubaya'ar Abubakar haka kawai ta zo kuma ta tabbata" sai Umar ya fusata ya ce "Zuwa dare zan miqe a gabansu na gargade su, mutanen da suke so su qwace lamari daga hannun masu shi" sai Abdurrahman ya ce "Sarkin muslmi kar ka yi haka, irin wannan taruwar ta aikin haji takan taro har da gidadawa da marasa hankali... ka dan dakata har sai ka koma Madina

"Can gida ne na hijira da Sunna, inda masu fahimta da manyan mutane suke, ka fadi abinda za ka fadi masu ilimi za su saurare ka su saka zancen a inda ya kamata" Umar ya ce "Amma in sha Allah zan yi haka a zamana na farko da zan yi a Madina (Buhari 6442), da wannan dalibin ilimi zai dauki haske, duk abinda za ka yi ka sa maganin hangen nesa ka duba tukun ka gani, bayan ka yi me zai faru? Abu ne da kowa ya ke buqata matuqar zai janyo hakulan jama'a.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*

*Follow my Facebook page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
Post a Comment (0)