TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 6


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//06📿*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

GINSHIQI NA HUDU

*GUJE WA QOQARIN CIN NASARA*
Zai yuwu abokin tauna-taunanka ya dan baqanta maka rai, can sai kuma ya yi kuskure a maganarsa ko a wani abu da ya yi, kai kuma sai ka sami damar da zaka dauki mummunan mataki a kansa, ta wurin amfani da wannan abinda da ya yi, ba shakka wannan ma kuskure ne wanda zai iya kai mutum ga fadawa barna, dalibin ilimi ya yi qoqarin guje wa wannan don kamar taimakon daga addini ne amma a gefe guda nasara kawai yake nema ko ta halin qaqa.

Babban abinda mutum zai guda shi ne manyan abubuwannan guda 4 wadanda Annabi SAW ya tsoratar da mu a kansu ya ce "Dabi'u ne guda hudu duk wanda ya hada su to wannan zallan munafiki ne, wanda kuma yake da dayansu to fa yana da dabi'ar munafurci sai in ya tuba: In aka ba shi amana ya ci, in zai yi magana ya yi qarya, in ya yi alqawarin aminci ya kai farmaki, in kuma za a yi tauna-tauna ya muzanta mutum (Bukhari da Muslim) ba abinda yake yawo tsakanin masu jagoranci kamar wannan masifar, qarya ta yi yawa a ko'ina, kuma duk qoqarin cin nasara ne ko muzantarwa.

Wallahi ina ji ina gani wani malami a gabammu yake cewa "Mutuwar wani babban malamin Izala an rufe shi ba kai, 'yan sikire sun cire kan, shi ya sa aka qi yarda mutane su ga janazar, a wajen taron Maulidi ya fadi, a gaban manyan malamai har da wadanda ake gani wayai ne, ba wanda ya ce wani abu sai mamaki ake ta yi da wasu ke yin Izala, na karanta bayanin wani a fesbuk da yake rantsuwa wai matar Zazzaki mazinaciya ce, nakan yi jayayya da Shi'a ga wanda ya san ni, amma wallahi ban gasgata ba, me yake nema da har sai ya yi wannan maganar?

Na ga wanda ya yanko kan malam Jafar ya dora wa wani da ya rungume wata mata, me yake nema anan, lada a wurin Allah? Na ga maganganun da ake liqa wa Inyasi, ko hoton kansa da ake gutsurowa a dora wa wani fasiqi, duk irin wannan bai yuwuwa mutum ya ce addini yake yi wa hidima ta hanyar fasiqanci, don 'yan Shi'a ba sai na yi maganarsu ba, tunda sahabbai ma ba wata qima suke da ita a idanunsu ba bare kuma wani salihin bawa da ake yi masa tunanin alkhairi.

Muzanci a wancan hadisin na sama yana nufin ne a wurin tauna-tauna ka jingina wa mutum abinda bai fada ba ko bai aikata ba don dai kawai ka ci nasara a tattaunawarka shi kuma ya kunyata, na karanta wadanda suke ce wa wani babban malami Bamu'utazile, wasu kuma da duk wani dalibin ilimi ya san su aka ce 'yan Ikhwan ne, don dai kawai a dusar da haskensu, wasu aka jingina musu tsanani a addini don a baqanta su, abin takaici galibin masu yawo da irin wadannan maganganun daliban ilimi ne, kai na ga wadanda aka ce 'yan Shi'a ne, tare da bayyanar cewa su suke yaqi da Shi'ar kai tsaye.

To in dai mutum ya sifantu da dabi'un wadancan kuma yake ganin cewa yana qoqarin daukaka addini ne haqiqa ba a daukaka addini da qarya, da ha'inci ko muzanta wani, abinda muslunci ya zo da shi shi ne dasa kyawawan hali, da ayyuka masu kyau, sam addini tun farkonsa bai sanya munanan abubuwa ko haramtattu su zama hanyar daukaka addini ba, shi ya sa Allah SW ya fadi qarara a suratut Taubah 119 ya ce ((Wadanda kuka yi imani ku ji tsoro Allah ku kasance da masu gaskiya)), wani sa'in in ka yanko qaryarka dalibinka ba wawa ba ne ya san qarya kake yi, muguwar biyayya ce kawai za ta hana shi bayyana maka, kar ka bari ya riqa ganinka tsirara.

GINSHIQI NA BIYAR

*SAKIN HANYA DABI'AR DAN ADAMCE*

Sabani a fahimtar abu, ko sanin hukunce-hukuncen shari'a abu ne da wani ya fi wani, qwaqwalwarmu ba guda ce ba, haka Allah SW ya halicce mu kuma ya fadi a Qur'ani ya ce ((Da Ubangijinka ya so da ya sanya jama'a a matsayin al'umma guda, haka za su yi ta samun sabani, sai dai wanda Ubangijinka ya yi masa rahama, da haka ya halicce su, maganar Ubangijinka ta riga ta kammala tabbas Zan cika Jahanna da aljanu da mutane gaba daya)) Hud 118-119

Ibn Taimiya yake cewa "Samun sabani a tsakanin mutane wani abu ne da ya zama dole wanda babu makawa saboda fifikon manufofi da fahimta da saurin gano abu, amma abinqi a ciki shi ne abka wa wasu da wasu ke yi da nuna musu qiyayya, da a ce sabanin bai kaiwa ga rarrabuwar kai da kafa qungiyoyi, ya zamanto cewa masu sabanin kowanne manufarsa dai da'a ce ga Allah SW da manzonsa da ba zai wani cutar ba, domin abu ne wanda duk yadda 'yan adam suka yi ba za su iya goce masa ba".

Ya ce " Idan dai asalin abida ake tattaunawa daya ne, abinda ake nema daya, hanyar da ake tafiya a kai daya ba wani sabanin da za a samu, ko an samun ma to kamar yadda ya gabata ne ba zai cutar ba, kamar dai yadda hakan ta riqa faruwa tsakanin sahabbai, don asalin abinda suka riqa gina lamuransu guda ne, shi ne littafin Allah SW da Sunnar ma'aikinsa, manufar guda ce, ita ce biyayya ga Allah SW da mansonsa, hanyar guda ce wato dubi ga ma'anonin Qur'ani da Sunna, da gabatar da su a kan duk wani zance, ko ra'ayi, qiyasi ko wata biyyaya ta shugabanci (As-Sawa'iq 2/519)

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
Post a Comment (0)