TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 7


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//07📿*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

*GINSHIQI NA SHIDA*

YA MUTUM YAKE?

Wani abu kuma mai matuqar mahimmanci shi ne a lura da mutum da kuma yadda yake, gaskiya ba daidai muke ba har a fagen fahimtar mas'alolin ilimi, koda kuwa qwaqwalwarmu na aiki iri guda, bare kuma akwai wasu 'yan abubuwa da ya kamata a ce an dan lura da su, misali: Ina da qwaqwalwa ba 'yar qarama ba, kusan duk littafan da babammu yake koyar da su na haddace tun ban kai shekara 25 ba, rayuwata ta qare ne a karatu da karantarwa, tabbas a fagen ilimi in abu kadan ne nake ganin ban sani ba, sai dai duk da haka tunda iyakacina kenan qauyemmu ko gaban babammu ya kamata na yi wa kaina adalci.

Misali Abu-Hanifa, da Malik ya zo a bayansa, an fadi cewa Malik din ya fi shi, kasantuwar koyarwar sahabbai da tabi'an da ta wanzu a wurin, an kuma yi maganar fifikon Shafi'i saboda karatun da ya yi a wurare daban-daban ciki har da Malik din kansa wanda ya sa koyarwar ta fadada sama da ta Malik din, Ahmad bn Hambal an yi bayanin malaman da ya bi su da wuraren da ya taka kafin ya harhado wadannan hadisan da ya koyar da mu, kenan maganar Allah SW da yake cewa (Ku yawata a bayan qasa ku ga...) ta nuna cewa yawatawar wani nau'i ce ta karatu.

Kenan ni da na yi karatu a gaban tsohona ko a qauyemmu ban yi kamar wanda ya fita ya je Saudiya ya yi karatu a gaban manyan malaman duniya da suka rubuta littafan da nake sayowa na karanta a gida ba, su sun zauna a gaban malaman an koyar da su, sun yi tambaya an ba su amsa, qila ma sun karanta ba su fahimta ba an yi musu qarin haske wanda ni ban sami wanda zai qara min ba, in na fito na ce musu batattu kamar ban fahimci abinda kalmar ma take nufi ba kenan, ban nufin dole sun fi kowa tunda sun je can, manufata dai dole a sami abinda za a yi qiyasi da shi.

Allah SW bai yi mu daidai ba kamar yadda muka karanta a baya, hatta wurin zaqulo hukunci, qila mutum ya kalli dan tsukinsa inda ya taso ba tare da kula da cewa duniyannan na da fadi ba, Allah ya halicci mutane a surori daban-daban, kowa da iyakarsa, da fahimtarsa, wannan ne dalilin da ya sa ake samun sabani a wurin fahimta, wasu da dama sukan yi jayayya ne gwargwadon fahimtarsu ba don barna ba, sau da yawa ma hujjar da za ka kawo musu ita za su kafa maka, kuma su ce su ke da ita ba kai ba, sai a tattauna har su gane ba a tilasta su ba ta hanyar muzantawa.

Ibn Taimiyya RL yake cewa "Ba fa duk wanda zai yi ijtihadi ya kawo hujja ne yake tabbataccen wanda ya san gaskiya ba, kawai dai ba wanda ya cancanci azaba ne in ba wanda ya bar abinda aka ce a yi ba, ko ya yi abinda aka hana, wannan ita ce maganar malamai da shugabannin addini, kuma ita aka sani ga magabata da daukacin musulmai (Majmu'ul Fatawa 4/209)" Ilimi dai yakan tabbata ne da samuwar wasu abubuwa guda biyu; ko dai da abinda ya tabbata hujja da shari'a ta kawo a nassance, ko kuma bincike da fitar da hukunci daga nassi bayan fahimtarsa, irin wannan qarfi na fahimta kuwa ba daidai yake da qarfin jiki ko yawan shekaru ba.

Da yawa za ka ga wani dalilin in aka sami mai kaifin hankali da hangen nesa ya fitar da shi sai ka ga an amfana da shi an sami gamsuwa, in wani da bai kai shi ba ya zo sai ka ga shi kansa bai fahimce shi ba bare ya gamsar da wani, duk da haka sai a yi masa hanzari saboda wasu dalilai, kodai qwaqwalwarsa ba ta iya taimakonsa wurin zaqulo daidai ba, ko kuma karatun nasa bai yi nisan da zai iya hango hukuncin ba, ko ba ma abinda ya karanta kenan ba shi ya sa bai kallo daidai din ba, ko akwai abinda yake fisgarsa ne ya kasa tsayawa a kan ma'anar da ake buqata, sai a gyara masa in ba zai yi girman kai ba.

Akwai lokacin da Ibn Taimiyya yake yi wa Razi raddi a wasu littafai nasa, ya kawo masa wata magana ya yi masa raddi ya yi gaja-gaja da ita, sai kuma ya yi masa uzuri ya ce "Ba da gangan ya yi don ya taimaka wurin yada barna ba, ya yi ne gwargwadon fahimtarsa da kuma bincikensa" ya ce "Za ka sami mai munana masa zato ya ga kamar da gangan yake yada barna kuma ba haka ba ne, ya yi magana ne gwargwadon fahimtarsa, karatunsa da bincikensa a duk mas'alar da ya zo kai".

Ya ce "Idan wannan raunin shi ne iyakar abinda zai iya ba zai iya kawar da shi ba to gazawarsa za ta zama hanzari, Allah ba zai azabtar da shi ba don ijtihadi ya yi (Fatawa 5/561-563)" da wannan za mu fahimci cewa kowa fa da irin qarfin fahimtar da Allah SW ya ba shi wurin fahimtar nassi da hukunce-hukuncen shari'a, duk wanda zai yi tauna-tauna da wani ya kamata ya dubi wannan lungun ya yi wa mutum hanzari, duk da haka ya fito da gaskiyar ba tare da muzanta abokin tauna-taunarsa ba.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
Post a Comment (0)