*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//08📿*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
*GINSHIQI NA BAKWAI*
DUBA HALI DA INDA MUTUM YAKE
Muslunci cikin yardar Allah ya yi fadin da yakai tsakanin qasar Sin wato Caina zuwa Amurka, a tsakiya matattaru ne kala daban-daban dake da al'adu mabambanta, wanda hakan ya haifar da wasu bambance-bambance a hanyoyin fidda hukunci a addini, har aka sami irin wannan bambancin a wurin tafsirin nassosi, da hukunce-hukuncen lamura, amma cikin yardar Allah SW wannan bai kai ga samun sabani a rukunnan muslunci ba, al'ummar musulmi duk sun hadu wurin cewa Allah daya ne, kuma sun tabbatar da cewa Annabi SAW manzo ne da Allah SW ya aiko shi ga mutane, haka tsai da sallah, ba da zakka, azumin Ramadana, aikin hajji, wadannan su ne rukunnan muslunci.
Al'umma sun sake haduwa wurin imani da Allah SW, da mala'ikunsa, littafansa, manzanninsa, ranar lahira, da kuma imani da qaddara, wadannan rukunnan imani ne, dukansu ake kira da rukunnan addini, lokacin da mala'ika Jibrilu ya zo wurin Annabi SAW ya tambaye shi su, kuma bayan ya koma Annabi SAW ya tabbatar wa sahabbai cewa mala'ika ne, kuma ya zo ne don ya sanar da su addininsu, banda wadannan rukunnan akwai wasu 'yan bambance-bambance daganan zuwa can.
Ibn Taimiya yake cewa "Musulmai tsakanin 'yan Sunnansu zuwa 'yan bidi'a sun yi ittifaqi wajen wajibcin yin imani da Allah, mala'ikunsa, littafansa, manzanninsa, da kuma ranar lahira, kamar yadda suka yi ittifaqi wurin imani da wajibcin salla, zakka, azumi da hajji, kuma sun yi ittifaqi kan cewa wanda ya yi biyayya ga Allah da manzonsa zai shiga aljanna ba za a azabtar da shi ba, wanda kuma bai yi imani da cewa Annabi Muhammad SAW manzon Allah ne ba wannan kafiri ne ba ko shakka, wadannan abubuwa su ne asalin addini da ginshiqin imani, duk wanda ke jingina kansa da muslunci ko imani ya amince da su, wani sabani da za su samu a kan hukunce-hukuncen da suka shafi uquba a Lahira ko fassarar ma'anar wasu sunayen Allah da sifofi, abubuwa ne taqaitattu in za a kula da abinda suka yi ittifaqi a kai"
Ya ce "Duk da cewa masu saba wa gaskiyar da ta bayyana qarara a Qur'ani da Sunna su ne mutane suka sani da 'yan bidi'a, kuma ake tabbatar da batarsu ba su da wata magana da za su gaya wa mutane yanke ta zama tabbatacciya ko a karbe ta ga jama'a, kamar Khawarijawa (Boko haram) 'yan qadariyya, 'yan Shi'a da sauransu, masu ilimi da riqon Sunna sukan yi fito na fito da su kan 'yan wasu abubuwa, sai dai kuma a qarshe duk wani abinda za a yi ja-in-ja a kansa akan koma zuwa ga Allah SW da manzonsa (Fatawa 2/130)"
Wata rana ina zaune sai ga qara an kawo wai wata mata tana neman izalantar da matan jama'ar gari, tana koya musu cewa su daura hannu a qirji ya yayin salla, har lamarin ya nemi kawo matsala tsakaninta da maigidanta, wani abokina kuma yana salla ya zauna a kan qafa, sai mai masallacin ya jira shi ya kammala, sannan ya ce masa daga ranar in zai yi salla to ya nufi wani masallacin ba wannan ba, har wayau, wani ya yi irin zamannan ne na jalsatul istiraha sai wani dattijo da ake jin maganarsa ya dakatar da jama'a bayan sallah ya ce to shi dai su suka karbo Izala daga malam Abubakar Gumi, aka lissafa shekarun sannan ya ce bai taba ganin irin wannan sallar ba, don har rabkanuwa aka saka shi, duk kuwa da cewa ba shi ne liman ko ladan ba, shi ma ya ce irin wannan sallar ba dai a masallacin ba.
Akwai taqaddama mai girman gaske tsakanin wasu al'ummar kan cewa akwai basmala a salla ko ba za a yi ba, akwai wadanda suke ganin mace za ta yi karatu a bayyane ne daidai da yadda kunnenta zai ji a duk inda ake bayyanawa, wasu na ganin ba wani dalili da zai sa mace ta yi wadannan karatuttukan a bayyane, sai maganar mace za ta iya yin limanci ta tsaya a tsakiyarsu aka ce i, wasu suka ce ba wannan dalilin, na ga masallacin da in dai mutum ya shiga ba hula komai girmansa sai sun maida ahi baya.
Wasu kuwa in dai kana son ka sami matsala da su to ka yi sallama biyu a cikin salla hagu da dama, suna ganin sallama daya ce da za a yi ta a dama, in dai mutum mutum ya sami kansa a irin wannan matattarar inda ya ga sabanin abinda ya saba, ko ma wanda bai taba gani ba to ya dan dakata kadan kafin ya kai ga ya tofa albakacin bakinsa, ya karanci mas'alar tukun, ya karanci irin mutanen, sannan ya zabi hanyar da zai isar da saqonsa, buqatarsa ba wai ya fadi abinda yake ganin shi ne daidai su dauka ko su bari ba, fatarsa dai duk a dawo ga abinda ake ganin ya fi dacewa da shari'a.
Akwai wasu abubuwan da sabani kan shiga qila saboda bambancin yanayi ne da mutane suka sami kansu a ciki, da yanayin wurin ma, in har zai yi magana to ya kula da dabi'ar wurin, Shaukani RL yake cewa "Zan gaya maka abinda za ka yi aiki da shi wurin kafa hujjar Allah: Kar ka faji'anci jama'a kai tsaye ta wurin ka kawo musu wani abu, sannan ka nemi su rabu da abinda suka riga suka saba da shi, a'a, ka lalubi wata hanyar cikin haquri yadda za ka iya janyo zuciyoyinsu zuwa ga abinda Allah SW yake so wurin bautarsa, ka kwadaitar da su irin ladar da masu riqo da shari'a suke samu, wadanda suke zabin hujjoji na shari'a ba wai ra'ayi ba, suke neman gaskiya ba bata ba (Ãdabut Talab wa Muntahal Adab p56).
Ibn Qayyim ya dauko maganar Malikiyya a kan al'adun mutane ya ce "Kar ka tsaya kan abubuwan da ka samu ko yaushe a cikin littafai, a'a, in wani ya zo maka daga wani wuri can, zai tambaye ka, kar ka ba shi amsa da irin al'adunku na yankinka, tambaye shi yankinsa tukun kai shi can kai masa fatawa da ita, ba da al'adunku dake littafanka ba, tsayawa cikin abubuwan dake littafai kadai rashin sanin manufofin malaman muslunci ne da magabata (A'alamul Muwaqqa'in 3/354)" kamar a ce wane ya ciyar da alkama, kai kuma ka ga sai dai alkamannan shinkafa ba za ta yi ba.
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa: Abulfawzhaan*