ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 6

*06→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*

*→Ma’anar luwadi da hukuncinsa:*

Luwadi shi ne: Saduwa da namiji ko mace ta dubura. A kan haka luwadi ya kasu kashi biyu: Babban luwadi, wanda shi ne saduwa da namiji ta duburarsa; karamin luwadi shi ne saduwa da mace ta dubura.  

*→Hukuncin luwadi:*

Luwadi da dukan nau’o’insa guda biyu haramun ne a Musulunci, saboda ba ya cikin hanyoyin da Allah Ya halatta wa bayinsa su biya bukatarsu daga gare su.

Allah Madaukakin Sarki Ya fadi irin azaba da bala’in da Ya saukar a kan wadanda suke luwadi a surori goma a cikin Alkur’ani: Suratul A’araf, daga aya ta 80; Suratu Hud, aya ta 76; Suratul Hijir, aya ta 58; Ambiya’i, aya ta 73; Furkan, aya ta 28; Shu’ara, aya ta 160; Nnamli, aya ta 54; Ankabut, aya ta 28; Saffati, aya ta 133da kamar, aya ta 33. 

A cikin wadannan ayoyi, za mu ga yadda Ubangiji Ya hada wa mutanen Annabi Lud (Alaihis Salam) azaba da bala’i iri-iri, Ya makantar da su, Ya kife gidajensu, Ya jefe su da duwatsu, Ya jefa su cikin wuta.

Haka nan ya tabbata a cikin Hadisin da Imam Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah suka rawaito, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Duk wanda kuka samu yana aikin mutanen Annabi Lud, ku kashe shi, ku kashe wanda ake yi da shi.”

Sahabbai sun hadu a kan hukuncin wanda duk ya yi luwadi shi ne kisa, sai dai sun yi sabanin yadda za a kashe shi:..
Zamu kwana a nan, a dakacemu

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 

Don kasancewa damu a Telegram sai a danna links din dake kasa 👇👇
https://t.me/joinchat/M_XPUBckMpCl_dPC-2MrVA 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)