TSIMIN KWARJINI


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Hada Tsimin Mai Haifar Ma Mace Kwarjini Da Kima_*

Wannan tsimi ne wanda yake da matukar mahimmanci musamman ga matayen da mazajensu suke yawan kuka na rashin jin dadi yayin saduwa ko kuma ita kanta sai taji kamar ana tusa ma mata ice a gaba, to yar uwa ga maganin matsalarki yar uwa.

 Wannan tsimi yana Karawa mace kwarjini da kima a wajen mijinta.

Zaki nemi wadannan abubuwan kamar haka;
* Yan shila guda biyu.
* Albasa fara.
* Gyadar mata.
* Furen zogale.
* Idon zakara.
* Kayan qanshi.
*Bayani;* Zaki dafa wannan ‘yan shila da wadannan da duk kayayaki zaki zuba a cikin tukunya da kike dafa yan shila, kuma wannan hadin shi akesu a fara karyawa da shi da safe kafin mutum ya ci abinci, Yana matuqar kara kwarjini da kima da kuma ni’ima ga ya mace. domin yana daga cikin abinda yake taka rawa muhimmiya ga ma’aurata.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)