*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Yadda Ake Hadin Ruwan Kwakwa_*
Ki fasa kwakwarki ki tsiyaye ruwan cikin kwakwar, sannan ki bare bakin bayan kwakwar ki goga kwakwar da ‘greater’, sannan ki markada a ‘blander’, sai ki zuba ruwa a kan markadaddiyar kwakwar ki tace ruwan ki fidda dusar. Da ma kin bare dabinonki cikin gwangwanin madarar ruwa daya. Ki jika dabinon ya yi laushi sai ki markada ya yi laushi sosai, sai ki zuba a kan ruwan kwakwar, sannan ki zuba ruwan da ki ka fasa kwakwar ya zubo a ciki. Ki zuba zuma da garin madara cokali uku a ciki, ki juya sosai. Ki sa a firij ya yi sanyi ko ki saka kankara. Idan ba ki son sanyi sai ki sha a haka. Ki yini ki na sha; kar ki barshi ya kwana. Hmmm zumdum! Ba zan ce komai ba, sai kin gwada kawai, uwargida za ki ban labari.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*