*MATA ZA SU IYA ZIYARTAR MAKABARTA !!*
*Tambaya*
Assalamu alaikum mallam, ina da tambaya akan ko ya halatta mata su ziyarci makabarta, don suyi addu'a ga magabatansu ??
*Amsa*
Wa alaikum assalam
Ya halatta mata su ziyarci Makabarta, amma kar su yawaita, saboda Annabi (SAW) ya la'anci mata masu yawan ziyarar Makabarta, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi !!
Annabi (SAW) ya wuce wata mace tana kuka a jikin Kabari, sai ya ce mata "Ki ji tsoran Allah, ki yi hakuri" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (1283), a cikin hadisin Manzon Allah bai hana ta ziyarar Kabari ba, kawai ya yi mata WA'AZI ne akan ruri da koke-koken da take yi, sannan Nana A'isha ta tambayi Annabi (SAW) game da addu'ar da za ta yi in ta je Makabarta sai ya koya mata, kamar yadda ya zo a Sahihi Muslim a hadisi mai lamba ta (974), hakan sai ya nuna mustahabbancin zuwan mata Makabarta ba tare da yawaitawa ba.
Hadisin da aka rawaito cewa Manzon Allah ya la'anci mata masu ziyartar Makabarta bai inganta ba, saboda a cikin sanadinsa akwai Salih Baazaam, shi kuma yana da rauni a wajan malaman Hadisi, kamar yadda Ibnu Abdulbarr ya ambata a Tamheed 3/234.
Don haka ya halatta mata su ziyarci Makabarta, saidai su kiyayi yawaitawa, saboda hadisin Farko da na ambata, da kuma ruri da koke-koke, saboda hadisin Bukhari da ya gabata
Don neman karin bayani duba: Almuhallaa 3/388 da kuma Almajmu'u 5/310.
Allah ne mafi Sani
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*
29/05/2020
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
Ku Danna link din dake Qasa don kasancewa damu a shafin telegram👇
https://t.me/miftahul_ilmi
→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su shiga ta nan su aika da cikakken suna 👇
https://wa.me/2347036073248