BAYAN GAMA JININ HAILA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Hanyoyin Da Ya Kamata Abi Bayan Gama Jinin Haila_*

Bayan kin gama jinin haila yana da kyau ki samu ganyen magarya da turaren miski bayan gama wankan tsarki sai ki samu aluf da lemun tsami ki tafasa idan ya sha iska sai ki wanke kowane lungu da sako na cikin gabanki, domin yin amfani da aluf da lemun tsami zai tsabtace miki gabanki ya wanke duk wani sauran datti dake cikin gabanki, ya kashe miki kwayoyin cutar dake da akwai a gurin, bayan wannan sai ki dauko ganyen magaryanki da kika jika shima ki tafasa, sai ki kara wanke kowane lungu da sako na cikin gabanki, a nan hikimar yin amfani da ganyen magarya shine duk maccen da take amfani da shi babu wata macen da zata kai ta daraja a gurin mijinta, sai dai idan ita ma tana amfani da ganyen magaryar.

Ba dole sai kina jinin haila ba zaki tsaftace gabanki domin akwai wasu dalilan da suke tarama mace datti a gabanta kamar su;

* Tafiya mai nisa 
* Yawan zama ba wando.
* Wanke gaba da sabulu
* Sa wando jikakke
* Mace mai jiki da yawa
* Lokacin zafi
* Yawan tsarki da ruwan sanyi
* Masu yawan sa wani abu gaba na matsi (inserting)
* Masu yawan sa yar yatsa a gaba. Da dai sauransu, zaki yi amfani da shi, bayan kin gama tsaftace gun da abubuwan da aka ambato a baya sai ki dauko turaren miski ki rinka dangwalawa kina sanyawa a gabanki.


Wabillahi Taufiq.


Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*


Post a Comment (0)