DAGA ZUCIYATA 02

DAGA ZUCIYATA 02

Komai na yi ban burge ba
Komai na yi ban fa iya ba
Ko na yi ma ba za su yaba ba
Kuma ba za su koya min ba
Komai indai nawa ne ba sa so ba.

Ya kuke so ne wai na yi?
Mai kuke so ne wai na yi?
Ta yaya zan iya canja yanayi?
Shin ta yaya zan canja ra'ayi?
Bayan na san ni ne akan gaskiya?

'Yan uwa wasu na ƙina 
Duk da dai wasu na sona 
Abokai na ta guduna 
'Yan mata na shakka na 
Duk kawai saboda wai ina son gaskiya. 

Jama'a sun sani gaba 
Jama'a sun tasa ni gaba 
Jama'a na nuna min gaba 
Jama'a sun hanani ci gaba 
Jama'a kar ku manta Allah ba zai ƙyale ku ba. 

Na zamo kamar mujiya 
Wacce ta faɗa rijiya 
Tana faman ninƙaya 
Amma ta gaza kufcewa 
Kuma an gaza cetonta wai don ana tsammanin ba ta da gaskiya. 

Duk wanda shi bai da ra'ayi
Wannan ku kira shi gawayi
Girki da shi kawai za a yi
Bayan nan ba shi da amfani
Wannan shi ne zance na gaskiya.

Ka zamo mai tausayi
Zalunci sam kar ka yi
Hassada ita ma kar ka yi
Mugunta ma sam kar ka yi
In ko ka yi su tabbas ka kauce gaskiya.

Kada ka yawaita inkari
Ka zamo mai yin nazari
Ka zamo mai yawan uzuri
Ka zamo mai kuzari
Idan har ka yi hakan kana kan hanyar gaskiya.

Ka zamo jajirtacce
Ka zamo nagartacce
Ka zamo ingantacce
Ka zamo abin kwatance
In har ka yi hakan tabbas kana kan gaskiya.

Ba lallai sai ka soni ba
Ba lallai sai kin soni ba
Ba lallai sai kun soni ba
Kuma ba lallai sai kun ƙini ba
Amma kun gaza fahimtata shi ya sa kuka kasa gano wa ke da gaskiya.

Zan ci gaba...

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176

Post a Comment (0)