Waƙa: Mohenjo Mohenjo
Fim: Mohenjo Daro
Harshe: Hausa
Shekara: 2016
Sauti: A.R. Rahman
Rubutawa: Javed Akhtar
Kamfani: T-Series
Rerawa: A.R. Rahman, Arijit Singh, Bela Shende & Sanah Moidutty
• Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo Daro
Birnin Mohenjo Daro
• Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo Daro
Birnin Mohenjo Daro
• Miljul Aur Phir Mil, Haan Miljul Aur Phir Mil
Ku taru sannan ku ƙara haɗuwa waje guda.
• Bun Le Taana Baana, Tu Jaana Pehchaana
Ku ƙarfafa alaƙarku kamar yadda aka sanku a matsayin ɗaya a nan.
• Miljul Aur Phir Mil, Haan Miljul Aur Phir Mil
Ku taru sannan ku ƙara haɗuwa waje guda.
• Chand Aur Sooraj Dono Ne Dekha
Rana da wata sun kalli.
• Mohenjo Daro Mein Rangon Ka Mela
Bajekolin kaloli da ake yi a birnin Mohenjo Daro.
• Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo Daro
Birnin Mohenjo Daro
• Musha!
Hayya!
• Ye Jo Mela Hai
Wannan shagalin
• Musha!
Hayya!
• Ye Jo Khela Hai
Wannan wasan.
• Musha!
Hayya!
• Yahi Mela Yahi Khela Hai Jeevan
Wannan shagalin da wannan wasan su ne haƙiƙanin rayuwa.
• Musha!
Hayya!
• Arre Sun Sun Sun
Saurara! saurara!.
• Musha!
Hayya!
• Kahein Kisko Gun
Ku san wace irin nagarta ce anan.
• Musha!
Hayya!
• Yahaan Par Toh Dhani Hai Wo Jo Mann Ka Paaye Rang O…
Tajirai anan su ne waɗanda su ke da kaloli a zukatansu.
• Sabke Apne Chehre Apni Boli Ooo…
Kowa yana da irin fuskarsa da kuma harshensa.
• Par Sab Apne Hain Jaan Le Tu, Haan Jaan Le
Amma kowa anan makusanci ne, ku san da haka.
• Inko Gyan De, Inse Gyan Le, Vaapari Banja Re…
Ku basu ilimi, ku ɗauki ilimi daga gare su, ku zamo 'yan kasuwa.
• Pardesi Anjaane Sabhi Ko Hai Pukaare Mohenjo Daro
Wa baƙi, Wa waɗanda ba su sani ba, birnin Mohenjo Daro na kira ga kowa.
• Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo Daro
Birnin Mohenjo Daro
• Chand Aur Sooraj Dono Ne Dekha
Rana da wata sun kalli.
• Mohenjo Daro Mein Rangon Ka Mela
Bajekolin kaloli da ake yi a birnin Mohenjo Daro.
• Jo Bhi Yahaan Par Aata Hai
Duk wanda ya zo nan.
• Sunte Hain Woh Kho Jaata Hai
Na ji an ce ɓacewa yake yi.
• Nagri Jaadu Ki Hai Yeh Mujhe Hai Pata
Na san cewa wannan birni ne na tsafi.
• Jo Rang Hai, Jo Dhang Hai
Kalololin da kuma al'adun.
• Behka Bhi De, Behla Bhi De
Su kan iya bugarwa, da kuma ribata.
• Phir Bhi Mera Mann Kehta Hai
Amma duk da haka zuciyata na cewa.
• Yeh Jaadu Toh Hone Ko Hai…
Wannan tsafin bai soma ba ma tukun.
• Apne Ko Tu Khone Ko Hai…
Zan rasa kaina ba da jimawa ba.
• Musha!
Hayya!
• Ye Jo Mela Hai
Wannan shagalin
• Musha!
Hayya!
• Ye Jo Khela Hai
Wannan wasan.
• Musha!
Hayya!
• Yahi Mela Yahi Khela Hai Jeevan
Wannan shagalin da wannan wasan su ne haƙiƙanin rayuwa.
• Musha! X3
Hayya!
• Yahaan Par Toh Dhani Hai Wo Jo Mann Ka Paaye Rang O…
Tajirai anan su ne waɗanda su ke da kaloli a zukatansu.
• Chand Aur Sooraj Dono Ne Dekha
Rana da wata sun kalli.
• Mohenjo Daro Mein Rangon Ka Mela
Bajekolin kaloli da ake yi a birnin Mohenjo Daro.
• Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo, Mohenjo Daro
Birnin Mohenjo Daro
• Musha!
Hayya!
• Ye Jo Raat Aayi
Daren nan da ya zo.
• Musha!
Hayya!
• Wo Yeh Rut Layi
Ya zo tare da shi da wani yanayi.
• Musha!
Hayya!
• Yahi Rut Jo Tere Mann Mein Sapne Bo De
Wannan yanayin zai zai dasa mafarkai a zukatanku.
• Musha!
Hayya!
• Mera Kehna Sun
Ku kiyaye abin da zan faɗa.
• Musha!
Hayya!
• Wohi Rasta Chun
Ku zaɓi waccan hanyar.
• Musha!
Hayya!
• Wohi Rasta Jise Paake Tu Har Chinta Kho De
Hanyar da za ta kai ku inda za ku manta da duk wata damuwarku.
• Jag Mein Kuch Tu Chaahe Kuch Main Chaahun
A wannan duniyar kana muradin wasu abubuwa nima ina muradin wasu abubuwan.
• Sabke Sapne Hain Jaan Le Tu, Ho Jaan Le
Kowa na da mafarkai, san da hakan.
• Sapne Poore Ho Toh Yeh Thaan Le
Idan mafarkanka sun zama gaskiya, to ka ƙudurta.
• Jitni Hain Aashayein, Wo Puri Ho Jaayein
Fatan dukkan muradai za su cika.
• Tabhi Toh Sab Aayein Mohenjo Daro
Daga nan sai kowa ya ziyarci birnin Mohenjo Daro.
ƘARIN HASKE: Mohenjo Daro wani tsohon birni ne da ke lardin Sindh, Pakistan, kuma yana ne da Kogin Indus. Masana tarihi sun ce birnin ya kafu ne tun shekarar 2500 BC. Birnin yana ɗaya daga cikin manyan biranen wancan lokaci kuma ya na da mutane masu tarin yawa da kuma ci gaban zamani. Duk inda kuma aka ga na sa alamar ___ to alama ce da ke nuna cewa abinda su ke faɗi a wajen ba shi da wata tsayayyar ma'ana. Nagode
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
+2348185819176
Haimanraees@gmail.com