Wasu Mutane Huɗu
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.
Akwai wasu mutane huɗu, mai ƙaton ciki, mai siririyar ƙafa, mai ƙafafun itace, da mai ƙaton kai. Wata rana suka tafi shan kanya a daji, kowanensu ya hau bishiyar kanya. Suna cikin shan kanya, sai mai ƙaton kai ya hango mai gona yana zuwa, sai ya ce da sauran, “ga mai gona can yana zuwa”. Sai kowane ɗayansu takai-takai.
A garin sauka, sai mai ƙaton kai ya maƙale. Shi kuma mai ƙaton ciki a garin dariya cikinsa ya fashe. Mai ƙafafuwan itace kuma, a ƙoƙarin dirowa daga bishiya ƙafafuwan suka karye. Shi kuma mai siririyar ƙafa, a ƙoƙarin zuwa gida ya faɗa ramin gyare ƙafar ta maƙale a ciki.
Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.