FASSARAR WAƘAR SAJAN TERI DULHAN

🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

FASSARAR WAƘAR SAJAN SAJAN TERI DULHAN 

Waƙa: Sajan Sajan Teri Dulhan

Fim: Aarzoo

Harshe: Hausa

Shekara: 1999 

Sauti: Anu Malik

Rubutawa: Anand Bakshi

Kamfani: Saregama India Limited

Rerawa: Alka Yagnik

Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 

• Chandni Raat, Taron Ki Baaraat Hai

Dare ne mai cike da farin wata, akwai yiwuwar bayyanar taurari. 

• Dil Ki Mehfil Sajaane Mein Kya Der Hai, Kya Der Hai

Me yasa ake samun makara a yayin ƙawata ƙawar zuciya? 

• Dhadkanein Dil Ki Shehnaaiyaan Ban Gayi

Ƙarar bugun zuciya ya zama kamar sautin Shehnaai 
(Shehnaai wani irin kayan kiɗa ne da ake amfani da shi musamman a wajen ɗaura aure a ƙasar India) 

• Ab Toh Sajan Ke Aane Mein Kya Der Hai, Kya Der Hai

Me yasa aka samu makara a lokacin zuwan abin ƙauna? 

• Meri Zindagi Mera Pyaar Yaad Aa Raha Hai

Ina tuna rayuwar mutumin da shi ne masoyina kuma rayuwata. 

• Aanewala Hai Jo, Woh Yaad Aa Raha Hai…

Wannan da ya ke gab da isowa, ina tunano shi. 

• Sajan Sajan Teri Dulhan Tujhko Pukare Aaja…

Ya Masoyina, amaryar ka ta na mai kira a gare ka. 

• Aakar Mere Hathon Mein Mehndi Tu Hi Racha Ja…

Ka zo ka yi min ado da lalle a hannuwana. 

• Sajan Sajan Teri Dulhan Tujhko Pukare Aaja…

Ya Masoyina, amaryar ka ta na mai kira a gare ka. 

• Aakar Mere Hathon Mein Mehndi Tu Hi Racha Ja…

Ka zo ka yi min ado da lalle a hannuwana. 

• Aaja, Aaja, Aaja…

Taho, taho, zo... 

Ya Masoyina, amaryarka ta na mai kira a gare ka. 

• Aakar Mere Hathon Mein Mehndi Tu Hi Racha Ja…

Ka zo ka yi min ado da lalle a hannuwana. 

• Aaja, Aaja, Aaja…

Taho, taho, zo... 

• Payal Kajal Kangan Daaman Saare Tujhe Bulaaye…

Sarƙar ƙafa (a ƙafa ta) , kwalli (a idona), awarwaro (a hannuna), komai na kira zuwa gare ka. 

• Aaja Sajan Aaja Tere Apne Tujhe Bulaaye

Zo masoyina, makusantan 
ka na kira a gareka. 

• Aaja, Aaja, Sajan Aaja…

Zo, zo, Masoyina. 

• Mere Mehboob, Mere Humsafar

Ya abin ƙaunata, ya abokin tarayya ta. 

• Tujhko Kya Pata, Hai Tujhe Kya Khabar

Baka san komai game da wannan ba. 

• Ehsaan Tere Kitne Hai Mujh Par

Ina matuƙar godiya a gare ka saboda dalilai da dama. 

• Rab Pe Yaqeen Hai Jitna, Utna Hai Tujh Par

Irin yardar da na yi wa ubangiji, irin ta kaima na ke yi maka. 

• Aaja, Aaja, Aaja…

Taho, taho, zo... 

• Mera Mehboob Mera Sanam Aa Raha Hai

Masoyina, abin ƙauna ta yana zuwa. 

• Hum Toh Mar Hi Chuke They, Phir Janam Aa Raha Hai…

Na riga na mutu, damar sake yin wata rayuwar a gare ni yana zuwa. 

• Sajan Sajan Teri Dulhan Tujhko Pukare Aaja…

Ya Masoyina, amaryar ka ta na mai kira a gare ka. 

• Aakar Mere Hathon Mein Mehndi Tu Hi Racha Ja…

Ka zo ka yi min ado da lalle a hannuwana. 

• Aaja, Aaja, Aaja…

Taho, taho, zo... 

Cha Cha Cha Chann Chann… Cha Cha Cha Chann Chann

• Chunari Meri Rangeen Hui Hai Tere Rang Se Sajan…

Gyale na ya samu kala ne daga kalarka, ya masoyi. 

• Aakar Rang De Mera Ang Ang Apne Rang Se Sajan

Yanzu don Allah ka zo ka ƙawata dukkan jikina da kalolin ka, ya Masoyi. 

• Aaja, Aaja, Sajan Aaja…

Taho, zo, Masoyina. 

• Tumse Wafaein Bahut Main Karungi

Zan zama mai amana a gare ka har abada. 

• Kasam Teri Ab Yeh Dil Kisi Ko Na Dungi

Na rantse da sunan ka, ba zan ba wa kowa zuciya ta ba. 

• Aa Tujhe Bata Doon, Mere Dil Mein Kya Hai

Bari in faɗa maka abinda ya ke binne a cikin zuciyata. 

• Dil Lene Waale Tujhe Jaan Apni Dungi

Ya kai wanda ya sace zuciya ta, zan mallaka maka rayuwa ta. 

• Aaja, Aaja, Aaja…

Taho, taho, zo... 

• Dhadkanein Badh Rahi Hai, Woh Kareeb Aa Raha Hai…

Bugun zuciya ta na ƙaruwa yayin da yake matsowa kusa. 

• Khushnaseebi Banke Mera Woh Naseeb Aa Raha Hai…

Ƙaddarata na nan zuwa tare da fatattakin alherai. 

• Sajan Sajan Teri Dulhan Tujhko Pukare Aaja…

Ya Masoyina, amaryar ka ta na mai kira a gare ka. 

• Aakar Mere Hathon Mein Mehndi Tu Hi Racha Ja…

Ka zo ka yi min ado da lalle a hannuwana. 

• Chandni Raat, Taron Ki Baaraat Hai

Dare ne mai cike da farin wata, akwai yiwuwar bayyanar taurari. 

• Dil Ki Mehfil Sajaane Mein Kya Der Hai, Kya Der Hai

Me yasa ake samun makara a yayin ƙawata ƙawar zuciya? 

• Dhadkanein Dil Ki Shehnaaiyaan Ban Gayi

Ƙarar bugun zuciya ya zama kamar sautin Shehnaai. 

• Ab Toh Sajan Ke Aane Mein Kya Der Hai, Kya Der Hai

Me yasa aka samu makara a lokacin zuwa. abin ƙauna? 

ƘARIN HASKE: Wannan waƙa ce ta soyayya, kuma ta na bayyana irin tsantsar ƙauna da ke tsakanin masoya/ma'aurata tare da bayyana irin tsumaye da amarya kan yi kafin isowar mijinta, kuma na san cewa duk wanda ya kalla ko ya saurari wannan waƙa zai iya fahimtar hakan. Sai dai kuma an tafka manyan kura-kurai biyu a cikin wannan waƙa a inda ta ke cewa irin yardar da ta yi wa Allah shima irin yardar da ta yi masa kenan, lallai wannan saɓo ne domin yarda da wani da irin yardar da ka yi wa Allah dai-dai yake da ba wa wannan mutumin matsayin Allah wanda yin hakan kuma kafirci ne, sannan ta kuma cewa ta rantse da shi masoyin na ta wanda kuma Allah shi kaɗai ne ake rantsuwa da shi, shima wannan ba daidai bane gaskiya. Kuna iya tuntuɓar malamai da ke kusa da ku domin samun cikakken bayani akan hukuncin aikata irin waɗannan kura-kurai. Nagode 

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Post a Comment (0)