HAƊIN RUWAN DABINO

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Hadin Ruwan Dabino Don Samun Ni'ima Wadatacce_*

Yar uwa a har kullum babban burin matan aure ta zo mai gamsar da mijinta amma wannan daman ba zai yiwu ba sai kema kin taimaka ma kanki don samun wadataccen ni'ima.

Don samun ni'ima zaki iya hada wannan hadin da wadannan kayan hadin kamar haka;
* Ruwan dabino
* Ruwan Kwakwa
* Ruwan dusar kwakwa
* Madara gari
*Bayani;* Zaki samu dabinonki mai kyau sai ki jika shi, sai ki markada ki tace shi da rariya ita kuma kwakwar naki zaki gurza kwakwa sai ki markadata a blender sai ki tace ki cire dusar, sai ki hada ruwan dusar kwakwan da ruwan dabino sai ki juye ruwan kwakwa da ki ka fasa shima ki zuba akai, sai ki samu madarar gari ki dama ta da ruwa ki sai ki zuba akai ki juya, kisa a fridge yayi sanyi zaki iya sha safe da yamma.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)