TSUMIN KWAKWA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Tsumin Kwakwa_*

Yar uwa ga naki tsumin kwakwa don taimaka ma zamantakewar aurenki, yar uwa wannan hadin yana da kyau don saukar da ni'ima da gyara jiki.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Kwakwa
* Aya
* Dabino
* Danyen zogale
* Kankana
* Mazarkwaila
* Cukwui
* Nonon rakumi
*Bayani;* Zaki samu kwakwa kawai ki samu aya danya sai dabino ki cire kwallon da danyen zogale da kwakwa da kankana da cukuw sai mazarkwaila ki markadasu ki tace ruwan sannan ki dauko nonon rakumi ki zuba ki gauraya, sai ki dunga sha.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)