HARAMCIN YIN PRE-WEDDING A MUSULUNCI

HARAMCIN YIN PRE-WEDDING A MUSULUNCI
.
Pre-Wedding Pictures/Videos suna Daga Cikin Abinda Yanzu Mafi Yawan Al'Ummar Hausa/Fulani, Ina Nufin Musulmai, Suka Mayar Kamar Addini. 
Wannan Ko Shakka Babu Masiface Ga Duk Masoyinta Dama Masu Goyawa Abin Baya. Haka Kuma Sharrice Ga Al'Umma.

Pre wedding shi ne namiji da mace za su rinqa riqe Juna da rungumar juna ko sumbatar juna ana daukan su a hoto ko video, wannan yana Kasancewa ne duk kafin aure.

Wannan aiki Na pre wedding haramun ne, ba ya halatta ga muslimi ya yi shi, ko ya bada gudummawa wajen yin sa, ko da duk duniya ana yin sa. Saboda abubuwan da kefaruwa a lokacin yin sa.

1- TABA MATAR DA BATA HALATTA A GARE KA BA: Ya haramta ga namiji ko mace su taba juna, ba tare da aure ba, amma awajen Pre wedding picture wani zai dauki hoton nema yana sumbatar ta ko rumgumar ta, ko ya rike kugunta, Bayan kuma ba aure. Wannan bai halatta ba kuma koda ma ba sumbatarta yayi ba, haramunne yatabata.
ﻋﻦ ﻣﻌﻘﻞ ﺑﻦ ﻳﺴﺎﺭ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ " : ﻷﻥ ﻳﻄﻌﻦ ﻓﻲ ﺭﺃﺱ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺑﻤﺨﻴﻂ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺪ ﺧﻴﺮ ﻟﻪ ﻣﻦ ﺃﻥ ﻳﻤﺲ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻻ ﺗﺤﻞ ﻟﻪ " ‏( ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﻭﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ‏) ، ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﻤﻨﺬﺭﻱ : " ﺭﺟﺎﻝ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﺛﻘﺎﺕ ﺭﺟﺎﻝ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ " ‏( ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ 3/39 . ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺳﻠﺴﻠﺔ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ﺍﻟﻤﺠﻠﺪ ﺍﻷﻭﻝ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ 326).
"Da'a soka wa mutum allura ta bakin karfe akan sa, shi yafi masa alkhairi da ya taba matar da bata halatta a gare shi ba."

2- BAYYANAR DA TSIRECI: wajen daukan wannan Pre wedding din, hoto ne ko video dole sai matar ta bayyanar tsirecin ta da kwalliyar ta, ta nunawa duniya cewa ita fa, ta hadu, Mai kyau ce, Bayan musulunci Ya hana mace ta bayyanar da kwalliyar ta face GA wadansu mutane. Kamar yadda Allah yace:
" ﻭَﻗُﻞ ﻟِّﻠْﻤُﺆْﻣِﻨَﺎﺕِ ﻳَﻐْﻀُﻀْﻦَ ﻣِﻦْ ﺃَﺑْﺼَﺎﺭِﻫِﻦَّ ﻭَﻳَﺤْﻔَﻈْﻦَ ﻓُﺮُﻭﺟَﻬُﻦَّ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﺒْﺪِﻳﻦَ ﺯِﻳﻨَﺘَﻬُﻦَّ ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﺎ ﻇَﻬَﺮَ ﻣِﻨْﻬَﺎ "..... ‏( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻨﻮﺭ 31 )
"Kuma Kace ga muminai mata su rintse idanun su(daga Kallan mazan da na su halatta ba). Su kare farjin su kuma ka da su bayyanar da kwalliyar su, sai dai abin da ya bayyana ............"

3- RASHIN KISHIN JUNA: yin wannan aiki Yana nunawa cewa Ango baya kishin matar da zai aura Don haka zata iya cire hijabin ta, kirjin ta a bude, da hannaye ta da kafafuwan ta duk ta budewa duniya ta ganta, shi a wajen sa babu komai, ka ga baya kishin ta, ita ma bata kishin akan ta. Ya zama daiyus Manzon Allah yace daiyus ba zai shiga aljanna ba.
ﻋﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ " ﺛﻼﺛﺔ ﻻ ﻳﻨﻈﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﺇﻟﻴﻬﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ : ﺍﻟﻌﺎﻕ ﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻪ ، ﻭﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺍﻟﻤﺘﺮﺟﻠﺔ، ﻭﺍﻟﺪﻳﻮﺙ ".. ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺣﺴﻦ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻧﻈﺮ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ٢ / ١٤٥
Manzon Allah(S.A.W) ya ce: "Mutun uku Allah ba ya duban rahma gare su Ranar alkiyama: wanda ya ke wulakanta iyayan sa, na biyu mace mai kwaikwayan maza, na uku Addaiyus (mara kishin iyalin sa).

4- YADA ALFASHA: wannan Pre wedding din Yana daya daga cikin yada fasikanci a ban kasa, ta yadda mutum zai rungumi (ko kiss din) MATAR da bata halatta ba a gare shi, ya na nunawa duniya cewa yayi hakan ne don ku kalli fasikancin da ya yi.
ﻭَﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﺍَﻟﺪَّﺭْﺩَﺍﺀِ ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻪُ ﻗَﺎﻝَ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍَﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ } ﺇِﻥَّ ﺍَﻟﻠَّﻪَ ﻳُﺒْﻐِﺾُ ﺍَﻟْﻔَﺎﺣِﺶَ ﺍَﻟْﺒَﺬِﻱﺀَ { ﺃَﺧْﺮَﺟَﻪُ ﺍَﻟﺘِّﺮْﻣِﺬِﻱُّ , ﻭَﺻَﺤَّﺤَﻪُ. .
Manzon Allah(S.A.W) yace: "Hakika Allah Ya na kin Mutum Mai yada alfasha"

Allah ya sa mu dace
.
Shiek Lawal Abubakar Shuaib.
(Hafizahullah)

Post a Comment (0)