MAKOMAR JARUMI SHAH RUKH KHAN A BOLLYWOOD
Sunan Jarumi Shah Rukh Khan ba baƙon abu bane ga duk wani mahaluƙi da ke rayuwa a cikin wannan duniya kuma a wannan zamani, ko da yana kallon fina-finan Indiya ko kuma ba ya kallo. Domin a wani bincike da aka gudanar, an gano cewa kaso biyu na biyar ɗin mutanen duniya sun san da zaman jarumin, yayin da kaso biyu na mutanen duniya kuma suka kasance masoyansa ko kuma masoyan aikinsa, hasali ma dai, mutane da dama sun fara kallon fina-finan Bollywood ne saboda jarumin ko da kuwa ba shi ne jarumin da suka fi so ba. To me ya jawo hakan? Magana ta gaskiya ita ce tun da aka kafa Bollywood babu jarumin da ya kai SRK farin jini da yawan masoya a duniya, hakan da kuma kasancewarsa ƙwararren ɗan wasa kuma gwanin iya soyayya suka sa ya samu nasarori da dama da bai da tamka a masana'antar ta Bollywood. Kenan ba banza ba ake kiransa da 'Badshah of Bollywood' wato sarkin Bollywood.
To sai dai kuma, a cikin shekaru biyu zuwa uku da suka gabata fina-finan jarumin sun gaza taɓuka irin abin arziƙin da aka san fina-finansa da shi. Wani abun mamaki kuma shi ne, da yawan fina-finan sun yi matuƙar kyau kuma sun zo da sabon al'amari mai jan hankali (misali: Fan, Zero d.s) sai dai duk da hakan sun kasa taka rawar gani a tuƙullumar kasuwancin fina-finan Indiya. Sai dai kuma duk da haka, har yanzu fina-finansa ba su daina taka rawar gani a kasuwannin duniya ba, wanda hakan shi ne ke bada tabbacin cewa lallai jarumin ba ƙaramin shahararre bane.
To amma shin ko wannan rashin nasara da yake fuskanta a irin wannan lokaci zai iya zama sanadin suɓucewar kambun sarautar Bollywood daga hannunsa?
Magana ta gaskiya ita ce, ko baka son SRK ka san cewa ya cancanci wannan karaga, kuma komai rintsi da tsanani ba za a taɓa mantawa da shi a matsayin Sarkin Bollywood ba. To sai dai kuma fa, ina mai nadamar bayyana muku cewa wannan kambu na gab da suɓucewa daga hannunsa. Amma kuma, masu iya magana na cewa wani hanin ga Allah baiwa ne. A matsayina na masoyin SRK kuma wanda yake bibiyar lamarinsa fiye da yadda ake tsammani, nima na amintu da cewa lokaci yayi da ya kamata ya sauka daga kan wannan karaga ya koma kan wata. To amma, saɓanin abinda 'yan adawarsa suke tunanin zai faru na lalacewar aikinsa, watsewar lamuransa da kuma karyewar alƙadarinsa, ni ina hango zuwansa matakin da mutum ɗaya ne a tarihin Bollywood ya taɓa kaiwa kuma can ne zai fi dacewa da zuwansa.
Tabbas lokaci na gab da zuwa da Srk zai sauka akan karagar, amma ku sani, nasarorin da yake samu za su ci gaba da yawaita kuma zai kai wannan matsayi da nake hango masa ba da jimawa ba matuƙar yayi abu guda ɗaya jal! Wannan kuwa shi ne ya canja yanayin fina-finansa gaba ɗaya, ya koma bin wani sabon salo da tsari da zubi na musamman, matuƙar yayi hakan to in sha Allah zai ba magauta haushi kuma zai kai wannan matsayi da nake masa fata.
Ahalin yanzu Jarumi Amitabh Bachchan shi ne ake yi wa laƙabi da jarumin da ba a taɓa yin kamarsa ba a tarihin Bollywood da ma Indian Cinema baki ɗaya. To dama dai rayuwar nan ba ka cin lokacinka ka ci na wani, an yi lokacin da Amitabh shi ne sama da kowa amma yau wasu ne a wurin ba tare da darajarsa da kimarsa ta zube ba, hakan ya bashi damar kaiwa zuwa ga matsayin da yake a yau. To ga shi tsufa ya zo mai wanda watarana dai dole yana ji yana gani ƙila yin fim ɗin zai gagare shi. A ƙarƙashin wannan sai magana ta fara yawo kan in yau aka ce Amitabh ya ajiye kambunsa, wanene zai iya naɗa wannan kambun a damtsensa ya zauna daram? Shi ma jarumi Srk an yi lokacin da shi ne sama da kowa amma ga shi yanzu lamura sun fara ja mai da baya kuma hakan bai sa kimarsa da darajarsa ta zube ba, wanda hakan yasa na ke ganin lallai shi kaɗai ne zai iya maye gurbin jarumi Amitabh. Amma ga wasu misalai da zan bayar domin su gamsar da mai karatu.
KAMANCECENIYAR DA KE TSAKANIN JARUMI AMITABH BACHCHAN DA SRK.
1. Dukkansu baƙi ne a Bollywood, ma'ana ba su da uwa a gindin murhu a harkar. Ko da yake ana iya cewa ta wani fannin ma gara Amitabh da Srk.
2. Dukkansu sun fuskanci ƙalubale da ƙyama a farkon shigowarsu amma daga baya suka zama ababen so da koyi ga na baya.
3. Dukkansu fitattun jarumai ne da ƙasar India baki ɗaya ke alfahari da su.
4. SRK babban masoyin Amitabh ne kuma in ka yi nazari da kyau za ka iske ɓoyayyun kamanceceniya a yanayin fina-finansu.
5. Dukkansu sun taɓa yin aiki a gidan talabijin bayan fina-finan da suke yi 'yan ɗai-ɗai.
6. Dukkansu producers ne: wato masu ɗaukar nauyin shirye-shirye ne.
7. Dukkansu suna zaune ne yanzu haka a garin Mumbai.
8. Suna da laƙubba da suka samu a harkar fim da babu mai irinsu kuma suna kamanceceniya. MISALI: Amitabh Bachchan: Angry Young Man, Shahenshah of
Bollywood, Star of the Millennium, &
Big B.
SRK: King Khan, Badshah of Bollywood, SRK, King of Romance, "Brand SRK"
9. Dukkansu akwai butum-butuminsu a gidan tarihi na Madame Tussauds.
10. Dukkansu suna da lambobin yabo na Filfmare Awards guda goma sha huɗu daga ɓangarori da dama.
11. Kowannensu na da kamfanin shirya fina-finai. Amitabh ABCL Corp, Srk kuma Red Chillies Entertainment.
12. Dukkansu sun fito a cikin mutum uku da aka zaɓa a matsayin jaruman da babu kamarsu a ƙasar Indiya a bikin cikar harkar fim shekaru ɗari da farawa a ƙasar India tare da Dilip Kumar.
Wannan kaɗan kenan.
Wani abun dubawa kuma shi ne: jarumi Amitabh Bachchan ya taɓa shiga irin halin da jarumi Srk yake ciki a dai-dai irin wannan lokaci na faɗuwa da fina-finansa suka yi ta yi a wancan lokaci wanda shi ma dole ta sa ya je hutu daga yin fim har sau biyu, amma tun da ya dawo harkar a cikin fim ɗin Mohabbatein har yanzu nasara yake ci gaba da samu a kullum. Waɗannan da ma wasu dalilai su ne suka sa muke sa ran cewa, matuƙar jarumi Srk ya ci gaba da bin salo irin na Amitabh, to da yiwuwar in ya dawo fa babu mai dakatar da shi sai Allah. Kuma tabbas akwai yiwuwar shi ne zai maye gurbin jarumi Amitabh. Idan kuwa haka ta faru, to shi kenan daga wannan lokaci ya sha gaban takwarorinsa kenan wato Salman Khan da kuma Aamir Khan, domin yayin da za su yi ta karo da junansu akan wanene zai zama sabon sarkin Bollywood, shi kuma lokacin tuni ya koma amfani da suna irin su "The Big Khan", "King Of The Khans", "The Godfather Of The new generations" da makamantansu.
Fatan wannan almari ya kasance, domin kuwa in dai Srk bai cancanci wannan matsayi ba, to ban san kuma wani jarumi da ya cancanta ba.
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
+2348185819176
Haimanraees@gmail.com