WAYE ZAI MAYE GURBIN SHAH RUKH KHAN A MATSAYIN SABON SARKIN BOLLYWOOD?
Jawabai da na samu daga waɗanda suka karanta rubutuna da ya gabata mai taken MAKOMAR JARUMI SHAH RUKH KHAN A BOLLYWOOD ya tabbatar min da cewa tabbas mutane sun amintu da cewa Srk yana gab da sauka daga kan wannan karaga. To amma abin tambayar shi ne; waye zai maye gurbinsa a matsayin sabon sarki?
Na san cewa kowa yana da nasa ra'ayin akan wannan batu, to amma fa magana ta gaskiya ra'ayi kawai ba zai kai kowane jarumi kan wannan karaga ba face cancanta. Sai dai kuma mafi yawancin waɗanda ake tunanin za su iya hawa karagar nan ba su cancanta ba, don haka bari mu dube su da kuma abubuwan da ka iya hana su kaiwa ga wannan matsayi.
1. SALMAN KHAN: an sha kiran jarumi Salman Khan da suna king of Bollywood a wurare da dama, amma a ƙarshe dai kowa ya san wanene king of Bollywood na asali. Maganar gaskiya ita ce; 'Salman Khan zai iya zama king of box office amma bai dace da king of Bollywood ba'. Dalilai na kuwa su ne Salman Khan sam ba shi da zubi irin na shugaba, yana da zafin rai, yana da riƙo, bashi da aure kuma yana da saurin yanke hukunci sannan duk manyan jaruman Bollywood babu wanda ya kai shi shiga matsaloli, ko dai su zama na gaskiya ko kuma waɗanda aka ɗaura mai bisa zargi da hassada. Wanda kuwa duk ke fama da irin wannan al'amari to gaskiya bai cancanci shugabanci ba saboda gudun kawo ruɗani a tsakanin mabiya.
2. Aamir Khan: shi ma jarumi Aamir Khan an sha kiransa da sarkin Bollywood a wasu lokutan wanda shi kansa ya san cewa ba shi ne ke da wannan matsayi ba. Magana ta gaskiya ita ce: "Aamir Khan zai iya zama ƙwararren jarumin da Bollywood ba ta taɓa samun kamarsa ba kuma wataƙila ba za ta taɓa samu ba, amma ba zai iya zama sarkin Bollywood ba".dalilai na kuwa sun haɗa da: Aamir Khan ba ya shiga cikin mutane sosai, baya mu'amala da wasu daga cikin mutanen masana'antar, ba kowane taro yake zuwa ba ko an gayyace shi, yana da riƙon abu a rai da kuma kafiya. To kuwa babu yadda za a yi ace shugaba na da waɗannan abubuwan kuma a yi tunanin za a zauna lafiya tare da ci gaba, asali na dai ina da yaƙinin cewa a yadda yake da tsaurin ra'ayi ko ba shi matsayin aka yi da ƙyar in zai amsa.
3. Saif Ali Khan: masu kawo wannan jarumi ma a jerangiyar waɗanda za su ka iya maye gurbin Srk suna yaudarar kansu ne kawai.
4. Ranveer Singh: tabbas akwai mutane da dama da ke ganin cewa watarana Ranveer zai iya riƙe wannan kambu, to amma su sani cewa; jarumin ba shi da ƙwarewa, gogewa da kuma gwanancewar da zai iya riƙe wannan matsayi a yanzu gaskiya. Wataƙila dai nan gaba ya iya, amma a yanzu hawa wannan karaga ta fi ƙarfinsa gaskiya.
5. Ajay Devgn: lallai Singham of Bollywood ya taka matakai da dama na hawa wannan karaga, amma ƙarancin nasarorin fina-finansa suka sa ba za a iya bashi wannan karaga ba.
To duba da bayanan da suka gabata, zan so masu karatu su fahimci cewa: alamu sun fara nuna cewa bayan Shah Rukh Khan fa sarautar nan ta fi ƙarfin kowane KHAN da ke Bollywood a yanzu sai dai in fin ƙarfi za a yi. Ba kuma wai don shi laɗifi bane ko kuma don na yarda da nagartarsa fiye da ta kowa ba, amma tabbas jarumin yana da wasu abubuwa da babu mai irinsu face mutum ɗaya jal a kaf Bollywood a yanzu. Kuma wannan jarumi shi ne nake sa ran zai maye gurbin nasa. In sha Allah a rubutu na gaba za ku ji ko wanene shi. Nagode
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
+2348185819176
Haimanraees@gmail.com