TA YAYA?


TA YA YA?

Ta ya ya baka neman ilmin sanin Ubangijinka (Allah) baka da malamin da ka ke sanin addininka baka sauraren Karatukan malamai ba ka zuwa ka ji wa'azi sannan baka iya buɗe Alqur'ani ka karanta, baka san hadisan Annabi ba. Kuma kace zaka gudanar da rayuwar ka yadda ya kamata?? Duk zurfin ilmin ka na boko in dai ka rasa wancan to akwai matsala, dole gidadanci da rashin waye wa na addini yake shiga cikin al'amuranka ka sani ko baka sani ba. Sannan abu mafi tsoro dakushewan imani..

Allah Ta'ala ya tsare ya bamu ilmi mai amfani ya gafarta mana.

#Zaurenfisabilillah

https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)