```Assalamu Alaikum
Malam tambaya ta itace alokacin da nake haila zan iya kwanciya da alwala. Bissalam```
_*AMSA:*_
*******
ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،
Mai haila bazatayi alwala a lokacin da take cikin jinin al'ada ba, kuma koda tayi alwala din, toh alwalar bata inganta ba, saboda jini bai yanke ba, koda ace zatayi wanka a lokacin da jinin bai yanke ba, toh wankan baiyi ba, dole sai jini ya tsaya.
*Al-Hafiz Ibn Hajar* ya kawo zancen *Ibn Daqeeq Al-eid (rahimahullah)* Wanda yace:
*Imam Shafi'i* yace yin alwala kafin shiga barci bana matan da suke cikin haila bane, saboda da za'a ce tayi wanka lokacin da jinin bai dauke ba, yin wankan baya tsarkake ta daga jinin dake zuwa, Wanda kuma ba kamar mutumin da ke cikin janaba bane.
Amma idan jini ya dauke mata kafin tayi wanka saita bukaci yin barci, toh anan ya halasta tayi alwala.
_*(Fathul Baari, 1/395)*_
*Imam Nawawi* shima yayi zance makamancin wannan acikin littafin sa _*(Sharhul Sahih Muslim, 3/218):*_
Jama'ar mu (Malaman mazhabar Shafi'iyyah) sunyi ittifaqi akan cewa ba'a buqatar macen dake cikin jinin haila ko jinin biqi tayi alwala kafin shigar ta bacci, saboda alwalar bazata tsarkake ta ba, amma idan jinin ya dauke (kafin tayi wanka) toh ita kamar mai janaba ne.
_*(Sharhul Sahih Muslim, 3/218):*_
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_