BUDURCI NA 08


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

Fitowa ta daya=*{8}*

akwai tambayoyi da wannan littafin zai amsa,
 misali akwai masu tambayata ta internet tareda neman shawara akan acikin maza guda biyu wanne yafi dacewa mace ta aura amatsayin miji?

1=na farko namijinda ya sadu da mace kafin ayi aure,

2=na biyu kuma wanda yasan an taba saduwa da mace amma yace zai aureta ahaka
 
To idan ace dukkansu sunason auren mace kuma tanada zabi wanene daga cikinsu zata aura ta samu kwanciyar hankali?

to inaga ai wannan amsar a bayyane take abun dubawa anan da zargi da gori wanne zaki iya jurewa?

Kinsan dai mijin farko dole kullum zaiyita zarginki bazai taba sakankancewa ya Aminta dake akan shine kadai ya sanki a matsayin 'ya maceba,
wannan kuma yana ransa yayinda kema da zaran kin ganshi da wata hankalinki zai kasa kwanciya,

Shikuma miji na biyu kasan cewar yasan abunda ya faru dole kisha gori domin duk lokacinda abu ya hadaku kinsan me zai faru ballantana ya auro wata tofa saidai ki tushe kunnenki,

sai kuma wata tambayar wai mace tana rasa budurcinta ta wata hanya bayan saduwa?

Amsa…eh tabbas tana iya rasawa ta hanyar bude kafafunta ko hawa keke da tsalle da daukar kaya masu nauyi da yawan shekaru dakuma Rashin lafiya dadd sauransu,

 to amma ba daya yake da wanda aka sadu da itaba dalili kuwa anan fatar ce take iya fashewa ko tsagewa amma saduwa fatar tana fashewa sannan kofar ta bude kunga akawai banbanci don kuwa duk yanda mace tayi matukar ba saduwa tayi da namiji ba to babu yanda za'ayi mijinta yayi tunanin wani abu,
Muhadu agaba insha Allah,

Rubutawa✍🏼
Dr. Auwal Azare

*GABATARWA Miftahul ilmi*

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)