_*======BUDURCI NA=====*_
*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*
Fitowa ta daya=*{11}*
TAMBAYAN shine akwai wasu A'lamomi da mutum zai iya fahimtar Cewa anta ba saduwa da budurwa Wanda bata tabayin Aure ba,
Bayan Na Aure ta, Kokuma kafun Na Aure ta,
batare da Alaman daukan juna biyu ba?
Allah yasa tambayar danayi tana kan tsari Na gode.
Muhadu agaba insha Allah,
As'salamu Alaykum Warahmatullah Malam Dan Allah inaso a war waremun wan nan abin yana damuna,
Nayi aurene Amma koda nazo na sadu da Matar senaji kamar ba budurwa ba toh nake tunakode dama ba budurwa bace na aura, Dan Allah Malam atai maka a war waremun matsalar nan Dan naji wasu nacewa dole se anga jini?
Slm Malam Barka da war haka dafatan Malam yana cikin koshin lafiya,
Malam inada tambaya ne game da wan nan Darasi dakake gabatarwa na Budurci na, to tambaya ta itace wai shi budurcin nan da ake magana akan shi meye amfaninshi ga mazan ko mata?
Ina fatan Malam zai samu damar amsa tambaya ta Nagode.
Wadan nan sune kadan daga cikin irin tambayoyin danake samu game wan nan post da nake gabatarwa cikin ikon Allah,
*AMSA*
Da farko de yan uwana maza ina bamu shawara ya kamata mukoma makaranta mukoyi karatun Addini san nan mukoyi yadda akeyin aure amusulunci da kuma wa yakamata ka aura san nan ina yakamata kaje ka auro mace,
Haka itama yakamata tasan wane irin mutum yadace ta aura kuma ya zata zauna da mijin ta na Aure Dan Samun tsira duniya da lahira,
"Yan Uwa maganar gaskiya Babu yadda namiji zai iya gane wai Wan nan macen budurwa ce ko ba budurwa ba ta wasu alamu Dan duk alamun da zasu nuna maka ba hujja bane gareka ko kadan,
Kamar yadda mukayi bayani abaya yadda halittar maza take da Ban banci haka halittar mata take da Ban banci Wata Allah ya halicceta da babbar kofa kamar yadda wata take da karamar kofa wata kuma matsa kaiciya wata kuma arufe take ruf gaba daya to tayaya zaka gane ba haka Allah ya halicceta ba?
Dan haka ba aikinka bane tan tance wance budurwa ce wance ba budurwa ba,
kaidai kazama na kwarai se Allah ya hadaka da ta kwarai
Idan ko har kana zarginta toh bai kamata kaje gurin taba ballema ka Aure ta,
Muhadu agaba insha Allah,
*GABATARWA Miftahul ilmi*
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248