BUDURCI NA 1

_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

Fitowa ta daya=*{1}*

Da sunan allah mai rahma mai jinkai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga manzan tsira manzan Rahma Annabin mu Annabi muhammadu sallalahu alaihi wa sallama,

 ina farin cikin gabatar muku da dan takaitaccen littafi me muhimmanci ga rayuwar Aure da ma'aurata tareda addu’ar allah yasa albarka acikinsa,

Rayuwar Aure cikin farin ciki tareda samun kulawa ta soyayya da yabo akoda yaushe shine burin ‘ya mace,

 ma’ana shine abunda kowace mace tafiso fiyeda komai a duniya domin kuwa duk irin arziki da jindadi da mace ta samu bazasu bata nutsuwaba matukar ta rasa kwanciyar hankali tareda mijinta,

 kuma kowa ya sani kwanciyar hankali a gidan miji ba abune wanda sai mace ta isa aure ake zaunarda ita ayita mata fadaba,

Aa tun tana karama ake dorata akan hanya me kyau tayanda zatasan ita wacece ta hanyar bata ilimin addini dana zamani wannan shine ginshiki me samarwa mace farin ciki tareda miji a rayuwar aurenta,

Muhadu agaba insha Allah,
Rubutawa✍🏼
Dr. Auwal Azare

*GABATARWA Miftahul ilmi*

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Post a Comment (0)