BUDURCI NA 12


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

Fitowa ta daya=*{12}*

Abinda yakamata musani shine Wajen Neman aure nagarta ake nema asamu ba akasin ta ba,
Badede bane kaje Neman auren yarinya Amma kana tunanin budurwa ce ko ba budurwa ba, matuqar kasanta da tarbiya gidansu da tarbiya islama bai kamata kayi tunanin wani aibu gareta ba sede abinda ya bayyana gareka na zahiri,

Saboda kaima kanka inda za'a tsananta bincike na kwakaf se ansame ke da wata illa da bai kamata abaka ita aureba,

Zakaga wani yazo Neman auren yarinya Amma wai se tayi alwala ta dau Alqura'ni tayi rantsuwa dashi bata taba yin zina ba,
Wallahi haka wata ta aikomin da tambaya wai ya zatayi ta rantse ko kar ta rantse kuma ita bataso tayi masa karya, Dan Allah wayace se anyi haka ga mace san nan a Aure ta ?

Idan akace haka za'a yi toh kenan baza'a yi aureba Dan dayawa daga cikin Al'umma sun tabayin zina kodai ta kuruciya ko kuma a halin jahici,
Toh gaskiya ana amfani da zahiri ne ba binciken abinda ba'a sakaba,

Wan nan dalilan yasa wasu matan shiga cikin damuwa toh kenan su bazasuyi aureba tunda wani ya san su kafin mijin su na fari?

Hakan yasa mata dayawa fadawa Cikin wani Hali na ha'intar mazajensu da kutsawa cikin aikata haramun da jefa kansu Cikin halaka ta yadda suke kokarin samarwa kansu wani sabon Budurci tunda na gaskiya yatafi ,

Suna Amfani da wani Budurci na wucin gadi tunda burinka kaga jini shine kasameta budurwa,

Muhadu agaba insha Allah,

*GABATARWA Miftahul ilmi*

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)