BUDURCI NA 13


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

Fitowa ta daya=*{13}*
Wan tsakanin binciken da maza keyi na tan tance budurcin mace kafin Aure ko bayan aure yasabawa shari'a haka kuma ya sabawa tsarin zaman ta kewa na Al'ummar musulmi kai harda ma wadan da ba musulmi ba suna tsananta wan nan binciken duk da suma matan suna da nasu laifin ko ince sunfi kowa laifi,

Ta yadda dazarar tasamu Saurayin da take so toh fa zata sakar masa dukkanin jikin ta yayi abinda yagadama ya taba duk inda yakeso ajikinta daga nan har se ya Santa ya mace wai ita tana ganin ai Soyayya ce kada ta Hana shi ya juya mata baya yace baya sonta kuma daga karshe abinda zai faru k nan bayan ya Santa ya mace Allah ya kyauta Ameen,

Ada akasar Hausa idan akayiwa yarinya aure ana zuwane da farin kyalle a shinfida kan gadon angonci washe gari da safe se dangin mijin suzo su duba wan nan farin kyallen idan anga jini ajikin sa toh shikenan se acin gaba da bikin gidan miji wato gidan Amarya ana murna yasamu budurwa,

Awan nan lokacin gaskiya yakamata suna tsoron yin zina Dan gudun abin gori Dan idan tayi wasa bazata sake auruwa agarin ba kuma duk Dan ginta sun shiga uku da gori kai wata ba'a sake zuwa gidan Neman auren danginsu,

Amma koda zuwan shari'a akasamu Sunnah aka waye se yammata suka bude kafarsu suna tsula tsiyarsu san ransu saboda Basu san illar yin zinaba Musanman ga budurwa duk da yake ga kowace yana da illa, ganin cewa ba'a wan nan tan tance wa ayanzu anasu tunanin selokacin da tatashi yin aure seta gane ta tafka babbar asara Cikin rayuwarta,

Yayinda shikuma namiji zai yaudari yayan mutane yayita lalata dasu tunda shi ba'a gane Saurayi da wanda ba Saurayi ba,

Se lokacin da yatashi yin aure sekaji yana cewa aini mace tagari nakeso mai tarbiyya mai hankali mai kamun kai wadda bata Kula maza gaskiya ka makaro Dan Uwa ai kaima kasan karya kakeyi toh irinsune zakaji suna tsananta bincike kan wadda zasu aura gani suke itama kamar wadda suka lalata wani ya lalata ta ko zai lalata,

Muhadu agaba insha Allah,


*GABATARWA Miftahul ilmi*

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)