BUDURCI NA 3


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

Fitowa ta daya=*{3}*

Amataki biyar ne mace ke rasa budurci ta hanyar saduwa da namiji wanda idan ta tsallake wadannan to tabbas tayi gagarumar nasawa a rayuwar ta ta aure, Ace mijinta na farko shine zaisanta 'ya mace,

1=mataki na farko shine lokacinda take karama idan har bata samu kyakyawar kula da tarbiya ba,
 hakan yana faruwa da ita saboda kusan duka yara da ake yiwa fyade zakaga rashin kulawa ne tareda sakacin iyaye,

 kuma irin hakan yafi kasancewa idan yarinya bata gaban mahaifiyarta,

2=Mataki na biyu kuma talauci lokacinda mace keda bukatu na yau da kullum amma ya kasance babu wanda zai dauki nauyinta,

 Mata da yawa sun rasa budurcinsu ta wannan hanyar,

3=mataki na uku lokacinda mace ke tsakiyar Sha'awa babu abinda takeso fiyeda aure zakaganta da samari samada biyar,

To amma kuma babu wanda zata aura daga ciki saboda iyayenta karatu sukeso tayi hankalinsu baya kan wane hali take ciki da suwaye take mu'amala?

Ina take zuwa? Suwaye kawayenta?
Koda yake ana samun wanda mijin aurene bata samuba ko kuma iyayenta basuda halin yin aurenta,

to wannan halin ba karamin hadarine ga 'ya mace ba,

4=Mataki na hudu kuwa shine mace marar kamun kai idan har mace ta zama me mu'amala da maza dole hakan ta iya faruwa da ita,

Yayinda zakaga wasu acikin abunsha ake saka musu magani idan har mace tanason tsallake wannan matakin tofa dole ta zama me kamun kai tareda kiyaye kanta da mu'amala da maza barkatai,

5=a karshe kuma akwai soyayya yayinda mace ta hadu da wanda takeso takanji babu abinda zai nema wajenta ta hanashi,

 tofa anan idan akayi rashin sa'a wannan saurayin nata yaso yaudararta nanfa zai mata alkawarin zai aureta to amma bayan ta amince nan zata gane asalin shi wanene,

kunga wadannan matakai guda biyar sune sukeda muhimmanci a rayuwar mace da zaran ansamu matsala a daya daga ciki tofa nan mace zata shiga halin rashin tabbas,

Muhadu agaba insha Allah,
Rubutawa✍🏼
Dr. Auwal Azare

*GABATARWA Miftahul ilmi*

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)