*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 18```
.
RASHIN GIRMAN KAI
Na isa wata qasa a 2002 inda na kammala digirorina a 2015, idan muka lura da cewa na dan jima a can, kuma ko tun farko karatun ne dai ya kai ni, sannan a matakin digiri wanda ko kafin na tafi ina da diploma kuma na dan jima ina koyarwa wadannan abubuwa za su iya ba ni damar da zan dan lura da wasu abubuwa wadanda sun dan saba wa yadda na saba gani a qasata, ba ina cewa sun fi mu hikima ne da jajurcewa ba, amma akwai wasu abubuwan da in an koya za a iya magance zaman banza, bambadanci, ubangidanci, neman alfarma da qarfa-qarfa, a can ne na ga wanda yake aiki a gidan jarida da majalla ta qasa da rana, in dare ya yi ya koma wata jami'a a matsayin mai-kula da yara yana kwana da su, yana dan samun na cefane.
.
Na ga soja a matsayin major kuma malami ne a wata jami'a, na shiga ajinda da yake koyar da addinin kiristanci, tsakanina da Allah bayan na gabatar da wata qasida sai da ya nuna min cewa ban san komai a qasata ba, ni kaina na yarda da hakan, masamman irin hujjojin da ya bayar, na ji labarin wani babban sojan sama da yake koyar da konfuta a wata jami'ar, ni da kaina na taba ganinsa a cikin kaki ina ta mamaki, na ga wasu masu dafa abinci a wata jami'a ashe 'yan sanda ne, suna aikin ne idan sun cire kaki don su qara qarfin abinda suke samu a wata.
.
A lokacin da muke dalibai na ga wani ministan ilimi wanda shi ne shugaban tsangaya ta ilimi a wata jami'ar, akwai wani dan sanda da muka san shi, sai ga shi yana kamisho, ban sani ba in wannan yana da alaqa da tsaro ko baida shi, ina kuma da masaniyar cewa qasata ba ta ba da hurumin da ma'aikacin gwamnati zai yi aiki biyu ba, amma kuma ba a hanaka ka nemi na rufin asiri a wani wurin ba, babban abinda yake ba ni sha'awa da su shi ne babban aikin da kake yi ba zai hana su su yi wani da ake ganin qasqantacce ne ba, tabbas akwai masu yin haka anan amma ba su ne suka fi yawa ba.
.
Zai yi wahala mutumin da ya yi kansila a same shi ya koma ajinsa na furamare kamar yadda yake da, to bare kuma wanda ya hau matsayin shugaban qaramar hukuma, da ya koma aikinsa na baya ya gwammace ya riqa bin 'yan uwansa 'yan siyasa su ba shi ko su hana, matsalar da muke fama da ita kenan, na ga kansiloli a baya da suka riqa sayen filaye da gina gidaje suna wadaqa da kudi yadda suke so, abin takaici ba sa iya aiki da damar da suka samu ta wurin gina qaramin kamfani ko wata ma'aikata ko shagon kayayyaki yadda in suka sauka za su koma can don rufin asiri, da sun sauka da dan qaramin lokaci sai ka ga sun lashe abinda suka tara.
.
Wadanda suka sayi filaye, motoci da sauransu in ba sa'a aka yi ba nan da nan za su kadar da su su bi kan kudin su lashe, da a ce kansilanmu malamin makaranta ne, lokacin da ya sami kudinnan kamar ana zubo su da bakin qwarya sai ya sayi wani fili ya gina makaranta tunda ya san kan abinnan, yana sauka ya qara fadada ta ya sami hanyar da zai riqe rayuwarsa ya dauki wasu ma aiki, yau a ce mutum tela ne aka ciro shi aka nada shugaban qaramar hukuma, da sai ya yi kamfacecen shagon teloli, ya zuba kekunan da ba ko'ina ake samunsu ba, ya dibi ma'aikata, sannan ya yi ofis dinsa na masamman saboda ko-ta-kwana, yana sauka ya san inda zai je.
.
Hana qarya na ga wani kansila wanda tun asali shi manomi ne, dan abinda yake samu a gwamnatance ya riqa qara shi cikin abinda yake birnewa a qasa, ya qara zama babban manomi, koda ya sauka ba wani abu nasa da ya canja, don ko tun yana kai yakan dibi 'yan qwadago su shiga daji, nan ma ya taimaki wasu, duk da cewa rayuwa ta dan sauya da ya sauka din, amma bai wani shiga halin ni-'ya-su ba, wani tela da na sani ya sami aiki babba, kuma yana samun kudi ba shakka, a maimakon ya qawata sana'arsa ta farko ya habaka ta bai yi ba, a qarshe damar da yake da ita ta kubuce masa, har muka rabu shagonso ba a daina murza zare a cinya ba, bayan na ga wasu suna amfani da wani dan inji qarami.
.
Matuqar babban matsayin da ka samu a yau na dan wani taqaitaccen lokaci ne da yatsun hannunka za su iya qirgawa, me zai hana ka yi wani shiri da za ka dade kana jansa bayan saukarka ko bayan gushewar wannan damar? In ka yi hakan aikin da ka samu zai dada taimakonka ne zuwa ga nasarar da kake sa rai da ci a rayuwarka, tabbas wasu suna da tsari, sukan waiwayi halin da suke ciki kafin su sami kansu a irin wannan halin na yau, sukan yi tunanin cewa in fa suka sauka za su iya komawa gidan jiya, sai su yi wa kansu tsari.
.
In a baya mutum ya karanci likitanci ne amma bai fara aiki ba saboda halin da ake ciki na qarancin gurabun aikin, sai Allah ya tarfa wa garinsa nono ya sami wani muqaddashin qaramar hukuma na riqo, me zai hana ya ririta dan kudin da yake samu wurin gina qaramin asibiti, ya riqa kawo kayan da ake buqata a hankali yadda kafin ya sauka ya gama tanadar duk abubuwan da ake buqata? Da farko dai in ya sauka zai ci gaba da aikin da ya karanto a wurin da shi ne shugaba, sannan kuma zai samar wa bayin Allah da aikin yi, ga riba ga lada.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```