GUDUNMUWAR ILIMIN 'YA'YA MATA GA YANKIN AREWA 2

Arewa students orientation Forum!!!


"GUDUNMUWAR ILIMIN 'YA'YA MATA GA YANKIN AREWA"


Kashi na biyu(2)

•Tarihin Ilimin 'Ya'ya Mata a Nigeria

•Tarihin Ilimin' Ya'ya Mata a Yankin Arewa.

Fatima Umar Muhammad
Arewastf@gmail.com
_______________________________________________________

✔️Tarihin Ilimin 'Ya'ya mata a Nigeria.


Kafin nayi bayani akan gudunmuwar Ilimin 'ya'ya mata ga yankin Arewa akwai bukatar mu kalli shi karan kanshi tarihin Ilimin 'ya'ya matan dan ya haska mana ta yadda zamu fahimci gudunmuwar.

Ilimin 'ya'ya mata a Nigeria zamu iya cewa ya fara ne tun a Shekarar 1920 inda a lokacin muke da makarantun Primary Dana Secondary guda 25, Kuma uku ne kacal suke na mata zallah, sauran kuma duk na maza ne, a Shekarar 1949 Makarantun da aka warewa mata suka kai guda 8, a yayin da 49 suke na maza, kana, a Shekarar 1960 aka kara samarwa da matan makarantu guda 6, sai ya zama jimillar makarantun mata a wannan lokacin sun kai 14.
Duka Wadannan Makarantun suna karkashin kulawar Kungiyoyin Mishan ne (Missionaries Organization) da kuma turawan mulkin mallaka na Ingila (England Colonial Masters).

Bayan da Nijeriya ta samu 'yancin kai (Independence) a Shekarar 1960, gwamnatin tarayya ta bude Jami'o'i 5 da suka hada da:
1• Jami'ar Nsukka (1960)
2• Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria (1962)
3• Jami'ar Ile-ife (1962)
4• Jami'ar Legas (1962)
5• Jami'ar Ibadan (Wadda aka fara kafa ta tun a Shekarar 1948).

✔️Tarihin Ilimin 'Ya'ya mata a Yankin Arewa

Nijeriya kasa ce da ke da mabiya addinai daban daban, (Secular State) manyan cikin su su ne: Musulunci da kiristanci, wanda dadaddun addinai ne a Nijeriya.
Kuma tun daga wannan lokaci ake samun hanyoyin ilmantar da jama'a.
Alal misali: tun a karni na 14, (14th Century) lokacin da musulunci ya shigo arewacin kasar (Northern Region) ake koyar da jama'a harshen larabci ta yadda zasu iya karatun al-qur'ani da sauran ilimomin addinin Musulunci (Islamic Educations).

Wannan ya nuna cewa Ilimin Arabia (Arabic/Islamic Education) ya riga ilmin boko (Western Education) shigowa Najeriya.

A shekarar 1934 a lokacin Sarkin Kano Abdullahi Bayero aka fara gina makarantar koyon harshen larabci (Arabic School) a Kano, inda ake koyar da shari'ar musulunci (Islamic Law) da kuma yaren turanci (English Language) da lissafi (Mathematics).
Makarantar ta bunkasa sosai inda a yau ita ne ta rikide ta zama Jami'ar Bayero (Bayero University, Kano).
An kiyasce cewa a shekarar 1914 akwai makarantun
Arabiyya kimanin dubu ashirin da biyar (25,000) a fadin arewacin Najeriya.

✔️ILIMIN BOKO✔️

Ilimin Boko (Western Education) ya shigo Nijeriya ne lokacin da kungiyoyin mishan suka shiga kasar a tsakanin shekarar 1842 zuwa 1914.
Tun daga wannan lokacin aka gina makarantu ana daukar yara domin a basu ilimin bokon.

Suna koyar da darrusa 4 da suka hadar da: 
-karatu (Reading Skills)
-Rubutu (Writing Skills)
-Lissafi (Arithmetic) da
-Kiristanci (Christian Religious).
Sannan akan horar dasu ta yadda zasu samu aikin yi
kamar: Koyarwa (Teaching) wa'azi a masalattai da coci-coci (Preaching) da tafinta (Intermediary).
Sai dai Ilimin bokon bai samu karbuwa a arewacin Najeriya ba sosai a wancan lokacin, sakamakon tasirin da ilimin addinin musulunci yayi ga mutanen yankin, kuma su kayi amannar cewa Ilimin bokon zai gurbata masu addinin su.
Duk da dai tarihi ya nuna cewa da karfin tsiya aka rika kama mutane ana kaisu makarantun bokon da Kuma bayi (Slaveries) da ake turawa suna yin bokon.
Idan ana maganar ilimin 'ya'ya mata a arewacin Najeriya Kamar yadda muka fada a sama,tarihi ya nuna cewa an
fuskanci manya-manyan kalubale da suka hana a bai wa mata damar neman ilimin boko, wanda namijin ma ba'a bashi damar neman Ilimin ba bare kuma mace. Kai bama ilimin boko ba har na Addini mata basu samu damar neman sa ba yadda ya kamata, har takai ana yi masu take da cewa “Sabbi saukar Mata” Wato da sun kai Suratul-A'ala Shikenan sun bar karatu da neman ilimi. A wancan lokacin an fi mayar da hankali ne kawai wajen ganin an aurar dasu da zarar sun fara tasawa.
Kalilan ne suka samu damar kammala makarantar firamare ko sakandire, yayin da tsirarru suka je jami'a,amma suma yawanci daga dakin aurensu.


NB. Asof bata kar6ar kudin kowa gun wani ko Kuma a turamaku wani links. 

02/02/2020.
Post a Comment (0)