WAƘAR BAKANDAMIYA



WAƘAR BAKANDAMIYA

Da sunan sarki rabbana mai duniya
Al-kaliƙu wanda ya yo duniya
Ya yi ƙorama har da teku na maliya
Al-maliku kai ke mulkin duka duniya
Sunanka ne farkon faɗi kowace safiya
Kuma kai nake kira da yamma sakaliya.

Na yi yabo gurin Annabi Muhammadu
Da ya fi kowa bauta Annabi Hamidu
Ma'aikin Allah Sahibinmu Mahmudu 
Shalelen Ubangijina ya Ahmadu 
Allah ka ninka salatai a wurin Ahidu 
Manzonmu sha-kundum Mahmudu.

Waƙa ce zan rera wa Bakandamiya
Shafin yanar gizon ga na duniya
Da ya zamo abin son mutanen Ifirikiyya
Kuma sha ziyartar mutanen Nijeriya
Yau shafin ya shiga dukkan nahiya
Fatanmu ya zamo na ɗaya duka duniya.

Matattarar fasaha ce Bakandamiya
Tsangayar marubuta ce Bakandamiya
Sulkumin manazarta ce Bakandamiya
Kajar ɗalibai ce Bakandamiya
Shirinyar Facebook ce Bakandamiya
Kinin Google ce Bakandamiya.

Akwai malumma a shafin Bakandamiya
Mafakar ɗalibai ce Bakandamiya
Muna sada zumunci a Bakandamiya
Muna koyon ilimi a Bakandamiya
Akwai fa nishaɗi a shafin Bakandamiya
Komai an taskace kamar Wikipedia

Jama'a na yi kiranku maza ku garzaya
Shafin al'ajabin nan maza ku antaya 
Ko gida ko ofis ko akan hanya 
Kuna iya buɗe shafin Bakandamiya 
Sauƙi ne ya zo wa Hausawan duniya
Fatan alheri na ke yi wa Bakandamiya. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com

Post a Comment (0)