WARWARA DAGA FINA-FINAN BOLLYWOOD 01


WAR-WARA DAGA FINAN-FINAN BOLLYWOOD KASHI NA DAYA (PART 1)

By Abba India Dala..

Zan Fara Da Film din SUNNY DEOL me taken GADAR: EK PREM KATHA:
Akwai Wani Abu da Yake Faruwa Acikin Finan-finan Bollywood Wanda Najima Inaso Na Fara Haskakawa Mana Musamman Mu Kananan Yan Kallo Wannan Abin Nikaina Ya Shafeni Kafin Na Waye da Kallon Finan-finan Bollywood Watau Tun Ina Yaro Muna Daukar Sunny Deol Bashi da Film se Na Yakar Musulinci Bayan Gaba Daya Abinda Aka Nuna Acikin Fim din Ba Aikin Musulman Bane, Wani Abu da Yake Faruwa a Finan-finan Bollywood Game da Film din da Musulmai Suke Ta'addanci Shine Sam Babu Koyarwar Musulinci Idan Zamuyi Duba Da Film din GADAR EK PREM KATHA shine Kamar Yanda Duk Wani Cikakken Musulmi Yake Yanason Zaman Lafiya Kuma Baya Goyan Bayan Zalinci Ko Zub da Jinin Wadanda Basujiba Basu Gani ba, Sannan Musulmi Kullum Burinsa Ya Ga Ana Shiryuwa Ana Fahimtar Ingancin Addininsa da Samun Yawaitar Musulmai a Fadin Duniya Amma Shi Wannan Film Gaba Daya Se Musulman Ciki Suka Zama Masu Son Yawan Zub da Jini..

Sannan Wani Sin Me Jan Hankali da Ya Bayyana Manufar Su Musulman Ciki Shine Wajen da Aka Nuna Sunny Yazo Gabansu Mugyambo a matsayin Sune Musulmai Kuma Suna da Burin Indai Zai Zauna da 'Yarsu se Sun Kafa Masa Sharruda Ya Yarda To Maimakon Su Nuna Nasa Kyawun Musulinci Se Akayi Amfani da Tursasawa Domin ya Shiga Kuma Duk da Haka Akayi Nasara Akansa da Farko An Fara Yi Masa Tallan Musulinci Kuma Yace Ya Karba Amma Abinda Zai Bada Mamaki Se Aka Nuno Fuskokinsu Duk Babu Annuri Se Fushi da Mamakinsa Kuma Maimakon Indai Musilincin ne A Gabansu to Su Fada Masa Kalmar Shahada Ya fada a'a se Aka Nuna Se An Kara Takureshi Watau Bayan Yace Ya Karbi Musulinci Se Aka dawo Maganar Se Yace Se Pakistan Duk da Haka Ya Furta Se Pakistan Duk da Ba Kasarsa ta Ainihi Bace Bayan Ya Furta Aka Ce Ya Zagi Kasarsa ta India..

Abin Tambaya Anan Shine Duk Wani Musulmi Nagari Wanda Babu Wata Mummunar Manufa a Ransa Yasan Cewa a Kome Musulinci Shine Farko To Mene Dalilin da Ya Riga Ya Amince Zai Musulinta Kuma Zaizo ya Zagi Kasarsa ta India?

To Abin Dubawa Anan Shine Kamar Yanda Akan Samu Wasu Masu Kiran Kansu Musulmai a Baki Amma Babu Aikin Musilincin To Haka Ake Samu a Ko Ina Don Haka Su Musulman Wannan Film Basa Aiki Akan Abinda Musulincin Ya Koyar Se Na Son Ransu To Da Yawan Film din da Musulmai Suke Fitowa a Yan Ta'adda Munafikai ne Kuma Ana Samun irinsu a Ko Ina Kai dai Kawai a Matsayin ka Na Musulmi a Ko Ina Kake Kayi Aikin da Koyarwar Addininka Domin Ka Zama Izina Kuma Abin Nuni Ga Wasu Mabiya Addinan Kuma Su San Kyawun Addininka Wata Kila Hakan Yasa Kaja Hankalin Wasu Har Suyi Sha'awa Koda Baka Sani ba To Zaka Samu Lada.
ALLAH YA KARA DAUKAKA MUSULINCI DA MUSULMAI NA GASKIYA..

Kashi na 2 Yana tafe...
#AbbaIndiaDala
Post a Comment (0)