YARJEJENIYAR KOMAI DA RUWANKA


*TASKAR TARIHI [23]*

 ```📍 YARJEJENIYAR KOMAI DA RUWANKA``` 
 
Sababin wannan Yarjejeniyar; wani Mutum ne daga cikin Ƙabilar (Zabid) dake Yaman, ya iso Makkah tare da kayan Kasuwanci, sai ya siyar dasu ga wani Mutum mai suna Ass ɗan Wa'il mutumin da ake danganta shi da Ƙabilar Sahamawa, sai wannan Balarabe Ɗan Gari yaƙi yaba wannan Mutum haƙƙin shi na Kuɗin kaya, sai wancan Baƙo yakai kuka zuwa ga Jama'u-Jama'u na Ƙuraishawa, sai bai samu wanda zai taimake shi ya karɓo mishi haƙƙin shi a wurin Ass ba.

Sai ya hau saman Dutsen Abu Qubays, Ƙuraishawa kuma suna mazaunan su da suke hutawa, sai yayi musu Ihu domin a kawo mishi da zaluncin da akayi mishi, sai Zubayr ɗan Abdulmuɗallib (Wan Mahaifin Manzon Allah SAW) ya miƙe, yace wannan ba abun bari bane, sai Banu Hashim suka haɗu, da Zuhrawa, da kuma Taimawa, dukansu suka haɗu a Gidan Abdullahi ɗan Jad'an, suka haɗa kai sukayi rantsuwa da Allah sukace; zamu haɗa Hannunmu gaba-ɗaya tareda wanda aka zalunta, har sai an mayar mishi da haƙƙin shi, to sai Ƙuraishawa suka kira wannan irin Yarjejeniya _(Yarjejeniyar Komai da Ruwanka)_ suka ce; waɗannan Ƙabilu sun haɗa kai sun shiga al'amarin da ba ruwan su. 

Sa'an nan sai suka tafi wurin Ass ɗan Wa'il suka ƙwato wannan Kaya na wannan Baƙo suka damƙa wannan dukiya ga mai ita. 

Manzon Allah SAW a wannan lokaci yana Matashi mai Shekaru Ashirin Ya halarci wannan Yarjejeniya wanda da ita ne suka ɗaga kirarin Gaskiya sannan suka rugurguza duk wani ƙoƙari na Zalunci. Ana ƙididdige wannan daga cikin abubuwan da suka ɗaukaki Darajar Larabawa. 
 
Haƙiƙa Manzon Allah SAW Yayi magana dangane da wannan yarjejeniya yace; “Haƙiƙa na halarci wani zaman Yarjejeniya a gidan Abdullahi ɗan Jad'an, *wannan Yarjejeniyar tafi mun daɗi da soyuwa a Zuciya ta fiye da in samu Jajayen Raƙuma, da za’a kiraye ne zuwa ga irin wannan aiki na alheri a Musulunci dana amsa”.*

*✍ ANNASIHA TV*
(https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09)

https://t.me/AnnasihaTvChannel
Post a Comment (0)