JAMI'A A TAFIN HANNUNKA


"JAMI'A A TAFIN HANNUN KA"

Daga:
Shehu Rahinat Na'Allah
WhatsApp:- 08038463491
Call:- 08025498888
Gmail:- shehurahinatnaallah@gmail.com

JAMI'A A TAFIN HANNUN KA shiri ne da zai rika zuwa muku dan ya warware muku wadannan abubuwa da zan lissafa a kasa, sannan zan rika daukar su daya bayan daya inayin bayani akansu da kuma amfanin su, ko muhimmancin su a Jami'a, kai har ma da ayyukan su.

•GA ABUBUWAN KAMAR HAKA:

(A) MANYA-MANYAN MUKAMAI A JAMI'A

1• Visitor
2• Chancellor
3• Pro-Chancellor
4• Vice Chancellor (VC)
5• Deputy Vice Chancellor Academic (DVC Academic)
6• Deputy Vice Chancellor Administration (DVC Admin.)
7• Registrar
8• Librarian
9• Bursar


(B) MANYAN MUKAMAI A JAMI'A, A MATAKIN TSANGAYOYI

1• Faculty Dean
2• Directors
3• Head of Department
4• Level Coordinator
5• Faculty Board of Examiners
6• Senate Business Committee (SBC)
7• Departmental Board of Examiners 


(C) MANYA-MANYAN HUKUMOMI A JAMI'A

1• Council
2• Senate
3• Faculty Boards
4• Congregation
5• Convocation


(D) CIBIYOYIN GUDANARWA NA JAMI'A

1• Vice Chancellor's Office
2• Students Affairs Division
3• Development office
4• Information, Public Relations and Protocol
5• Academic Planing Unit
6• Management information system (MIS)
7• NUNets
8• Security Division
9• Strategic Planing Unit 
10• Registry Department
11• Registrar's Office:
(a) The Academic Division
(b) The Publications and Documentation Division
(c) The Housing & Passages Office 
(d) The Establishment office
12• The Bursary Department
13• Health Service
14• Center For Information Technology (CIT)


(E) KUNGIYOYIN DALIBAI A JAMI'A

1• Students Union Government (SUG)
2• Faculty's Association
3• Departmental Association
4• State Unions
5• Local Government's Union
6• Unions and Clubs

Domin samun Cikakkun bayanai akan wadannan mukamai da Hukumomi da kungiyoyi da suke a Jami'a to Ku kasance tare da AREWA STUDENT'S ORIENTATION FORUM

Nagode.




JAMI'A A TAFIN HANNUN KA

Kashi Na 01.

•Jami'a wuri ne na rashin tarbiyya

•Jami'a wuri ne na Kazo-nazo

• Me yasa ake tsoron auren Macen da take Jami'a
________________________________________________________

•SHIMFIDA:

Jami'a wani wuri ne da jama'a da dama suke ma kallon wuri na cikakken 'yancin yin abinda kaga dama (Total Freedom) ba tare da an takura maka ko matsa maka ko hana ka, ko tsangwama ba (Discrimination).

Atakaice, anai mata kallon wuri ne na rashin samun cikakkiyar tarbiyya kuma wuri ne na rashin da'a (Discipline) kazalika wuri ne da yake Lalata Samari da 'yan matan da suke karatu a wannan wurin (Jami'ar) sakamakon cikakken 'yanci (Total Freedom) da ake ganin suna da shi, Wannan dalilin ya sanya dayawa daga cikin iyaye sukan hana 'ya'yan su Cigaba da karatu mai zurfi na Jami'a don gudun lalacewar tarbiyyar su, kai hatta ma samari sukan fuskanci irin wannan matsalar (Dan ko ni Mai rubutu mama na tana shan yimun Nasiha akan na kula da kaina, na kiyaye mutunci na sakamakon taji ance wuri ne na rashin tarbiyya), haka ma wasu daga cikin 'yan bokon sukance ba zasu iya auren duk Macen da karatun ta yakai Matakin Jami'a ba, ko kuma gaba da Sakandare, (Tertiary Institution) saboda zargin rashin tarbiyya da suke yiwa matan.

Kamar yadda Dr. Nasir Ashir yake fada cewa aduk lokacin da akace matar Jami'a abinda yake zuwa zuciyan mutane Shine: "Wata mace wadda take rayuwar wayewa da tinkaho, ko mace mai rayuwa daidai da yadda zamani ya tsara ba addini ba" to ire-iren wadannan zargi (Allegations) suna cikin ummul-haba'isin hana mata karatun boko mai zurfi.

Alal-hakika kuma ba haka bane, Jami'a wuri ne na tarbiyya da Ilimi da wayewa da gogewa ta rayuwa, kawai ya danganta ne da kai dalibi yadda ka dauke ta.

Duk da cewa ba'a rasa bata gari masu irin wadannan mugayen halayen na rashin da'a amma kuma akwai dalibai na kwarai masu tarbiyya da tsoron Allah da kiyaye mutunci kama tun daga kan Musulman kai har ma da mabiya addinin kirista.

Saboda haka idan muka kalli Jami'o'in Nigeria kaf, misali irin Bayero University, Kano zamuga suna bada digirin su ne BASE ON CHARACTER AND LEARNING, dan haka ma Character din shine ya fara zuwa farko kafin Learning din. Bisa wannan idan kayi wani Abu na rashin da'a da tarbiyya Jami'a tana da hurumin ta kwace (Invalidating) shaidar digiri din da ta baka koda kuwa ka kai Shekara 50 da gamawa.

•ME AKE NUFI DA JAMI'A ?

Jami'a ko kuma "UNIVERSITY" "wata cibiya ce ta Ilimi da take bayar da Ilimi har zuwa Matakin sa na karshe"

Wasu kuma suna kallon Jami'a a matsayin "wani matattara ne na dalibai daban-daban, masu kabilu daban-daban, Masu yare daban-daban, jinsi daban-daban, ra'ayi daban-daban daga kowanne Sassa na duniya"

Wasu kuma suce: "Jami'a wuri ne na kazo nazo"

Aminu Ala kuma yana cewa: "Jami'a wani tushe ne na Al'umma wacce take fitar da duk wasu shugabanni na al'umma Kamar: Likitoci, Lauyoyi, 'Yan Sanda, da alkalai"

•MANYAN MUKAMAI A JAMI'A

• Visitor

• Chancellor

• Pro chancellor

• Vice Chancellor

• Deputy Vice Chancellor Academic (DVC Academic)

• Deputy Vice Chancellor Administration (DVC Admin.)

• Registrar

• Librarian

• Bursar

Wadannan sune mukamai mafi kololuwa a tsarin kowace Jami'a, dan haka a rubutun mu na gaba zamu dauki kowanne daya-bayan daya muyi bayanin sa da kuma aikin sa a Jami'a.

Bissalam
ASOF_2021
9th February, 2021.
Post a Comment (0)