No title

MACE ZA TA IYA ASKE GASHIN KANTA? 

*MACE ZATA IYA ASKE GASHIN KANTA?*


*Tambaya*


Assalamu alaikum. Malam gashin matata ne yake karyewa, musamman in tazo tajewa dayawa yana fita. Shi ne tace tana son ta aske don sabo yafito


*Amsa*

Wa alaikum assalam,
ya haramta ga mace ta aske gashin kanta saboda hadisin da Tirmizi ya rawaito cewa: "Annabi S.A.W. ya hana Mace ta aske gashin kanta".

Idan Mace ta aske gashin kanta zai zama ta Yi kama da Maza, Allah kuma ya La'anci macen da take kamaceceniya da maza kamar yadda ya zo a cikin hadisi.

Wasu malaman sun halattawa Mace ta aske gashin kanta don wani sabon gashin ya fito, idan wata lalura ta same ta kamar KORA ko kwakuyewar Kai, Ibnu Uthaimin ya ambata hakan a Fataawaa Nurun aladdarb 10/13 sannan Athram ya hakaito kwatankwacin wannan fatawar daga Imamu Ahmad.

Allah NE mafi sani

24/06/2017.

*Amsawa:* Dr. Jamilu Zarewa.
*Gabatarwa:* Abu- Unaisa.

👉🏾 Darussunnah Foundation, 07035888158.
Post a Comment (0)