RASHIN ADALCI A TSAKANIN 'YA'YA YANA JAWO FITINTINU


*RASHIN ADALCI TSAKANIN 'YA'YA YANA JAWO FITINTINU ! ! !*

https://chat.whatsapp.com/BsuVPYdzZY7C1Sv0lgoNES

*TAMBAYA*❓

As-salaamu alaykum Malam Allah ya kara maka imani da fahimta Tambayata itace Mahaifinane yake nuna banbanci a tsakanin mu sannan yana yawan zagin mahaifiyata musamman in 'kanne na sunyi masa laifi sai ya kama zaginta Sai na nuna masa rashin jindadina da wannan Al'amari har ya kai ga mun daga ma juna murya. Karshe sai ya fara yimin Allah ya isa yana tsine mun.

*AMSA*👇

Wa alaikum assalam Ya wajaba uba ya yi adalci a tsakanin 'ya'yansa, Annabi S.a.w. yana cewa : "Ku ji tsoron Allah ku yi adalci a tsakanin 'ya'ya yanku" Wannan ya sa lokacin da Sahabi Bashir ya yiwa dansa kyauta, ya nemi Annabi s a w. ya yi shaida akan haka, ya tambaye shi : shin Duka 'ya'yanka ka yi musu kyauta ? sai ya ce A'a, sai manzon Allah ya ce : Ba ka so su zama daidai wajan yi maka biyayya ? ba zan yi shaida akan zalunci ba". Bukhari da Muslim sun rawaito wadannan riwayoyi.
Yin adalci a tsakanin iyalai yana inganta tarbiyya, yana sanyawa su ji tausayin Uba bayan ya girma, yana kara musu hadin kai da son juna.
 Ya wajaba mazaje su Sani cewa : zagin matayansu ya sabawa ka'idojin sharia, kuma hanya ce ta tabarbarewar tarbiyya, domin Yaran za su rabu biyu, wasu suna bayan mahaifinsu, wasu kuma Babarsu za su ga ta yi daidai. 
Ya wajaba a tausasa harshe lokacin da za'a yi magana da mahaifi saboda Allah ya hana fadawa Uba kalma mara kyau ko yaya take, kamar yadda ya zo a Suratul Isra'i. 

Ba'a son ana yın muguwar addu'a ga iyalai saboda in aka dace da lokacin amsar addu'a za ta zamar masa matsala
Allah ne mafi sani. 

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)