SHARRIN SAƁON ALLAH


Sharrin saɓon Allah..✍🏼


" Sharrin sabo da saɓa wa Allah sababine na a saɓa maka "

Sam kada ka baiwa rayuwar ka da gaɓoɓin jikin ka su zamto da sakewa a saɓon Allah:

Sam kada ka baiwa wani ragamar jagoranji da zai abokanceka da saɓawa Allah :

Sam kada ka baiwa matar ka umarni da saɓawa Allah, son ta saɓawa Allah ke sanya a saɓa maka kaima :


Sam kada ka yadda da rinjayar da son abin halitta fiye da Mahalicci; son da kake yiwa matar so shine ke kawo saken sanya ka zamto sai yadda tayi da kai:

Sam kada ka bada damar sãbo ga mace ta zamto ita ke faɗa aji; hakan ke sanya 'ya'yan ta su rayu suna saɓawa umarnin ka, duk yadda zaka yi kuwa :

Sam kada ka sabar mata abinda ba zaka dore aiwatar mata ba, domin da rana ɗaya kace baza kayi ba, zata fara ƙirga wannan cikin takurawa.

Sam kada kayi wa mace sako - sako akan addini da ɗabi'un nagarta, zata ɗoru akan hakan kuma ta gadar dashi ga 'yayan ta :

Sam kada ka bari ta gano lago - na rauninka ga addinin ka, zata raina maganarka ta raina ƙurar ka, idan kuma har ta raina ka; rainin zai illatar da tarbiyyar yaran ka:

Sam kada ka yadda da bayyanar da akasarin sirrikan ka ga mace, kai dai raba ƙafa; akasarin mata ga gorantawa suke fallasa sirrikan su da na mazajen su.



👌🏼Amma ka sani ɗan uwa mace sitirarkace ba a bi mata ta qarfi, ita abokiyar cire kewa ce da lallami ake samun kanta, idan kuma ka cika zare ido sai ta zaune ka da tsoro.
Post a Comment (0)