CIWON CIKI YAYIN AL'ADA


*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*

Daga zauren
📌Albahral Ilmu🌴
:
CIWON CIKI YAYIN AL'ADA
(Mestrual Cramp): Dalilai da maganinshi
:

Ciwon ciki yayin al’ada dai wani matsala ne da yawancin mata ke fama da shi. Mafi akasari ‘yan matan da su ka fara yin al’ada sabo sun fi fama da shi. Idan mace na girma matsalan kan ragu, har in ma ta yi sa’a ta rabu da shi gaba daya.
.
Dalilin da ke kawo shi Matsuwar mahaifa (Uterus Contraction): A yayin da mace ke al’ada mahaifarta kan matsu sannan ya takura hanyar jinin da ke kusa da shi, wannan takurar na hana iskar oxygyn shiga mahaifar na kankanin lokaci. Wannan rashin iskar shi ke kawo wannan ciwon ciki.
.
Wasu da ga cikin wadanda suka fi fama da shi a cikin mata sun hada da:
'Yan mata kasa da shekara 20.
‘Yan mata da ke fara balaga daga Shekara 11 ko kasa da haka.
Zubar da jinni mai yawa yayin al’adar.
Rashin haihuwa.
     
Alamomin ciwon cikin kan zo da wa su abubuwa kamar haka:
Ciwon baya da cinyoyi.
Tashin zuciya da amai•
Hada zufa da Jiri•
Gudawa ko sakakken bayangida
Daurewar ciki (constipation)
Ciwon kai•
Lalacewar ciki (bloating)•
.
Wasu da ga cikin hanyoyin magance shi a gida Zama cikin ruwa mai zafi na dan lokaci (hot bath)
.
Yin shayin Albabunaj, safe da yamma ana Shansa da duminsa
.
Gasa kasar cibi da ruwa mai dumi ta hanyar amfani da ruwa mai zafi a gora ko tawul da makamantansu
.
Kokarin ganin likita in har abin ya tsawaita
.
Wasu daga cikin hanyoyin da za a bi don rage shi
.
Yawaita cin ‘ya’yan itace (fruits) da ganye (vegetables)•
Rage cin abinci mai maiko, abinci mai caffeine (sinadarin kofi) da gishiri da kayan zaki (sweet)•
Motsa jiki a-kai-a-kai•
Rabuwa da shan taba•
Rage shiga damuwa (stress)•

A karshe, duk lokacin da matsala ta dame ki kar ki zauna a gida. Ki yi kokarin ganin likita cikin gaggawa. Allah Ya kara mana lafiya.             
:
```Allah ta'ala yasa mudace```
.
© Abdulkadeer Umar Alshinkafawy 
:
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
--------------------------
•Ga mai sha'awar shiga Zauren 
📌Albahral Ilmu🌴

ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu
   
      07064746551
〰〰〰〰〰〰〰〰〰
 Daga Zauren
   📌Albahral Ilmu🌴🌴
        ​
Post a Comment (0)