TASKAR TARIHI 30


*TASKAR TARIHI [30]* 

📌 ```IRIN TSAREWAR DA ALLAH YAYI WA ANNABIN SHI TUN KAFIN AIKO SHI``` 
 
Rayuwar Annabi SAW kafin a aiko shi, ta kasance rayuwa ce Maɗaukakiya kuma mai daraja, Manzon Allah SAW Yayi samartaka a zamantakewa ta Jahiliyya, Jahiliyyar tana nan da Aqeedar ta kuma Annabi SAW Ya rayuwa a cikin wannan zamani amma aqeedar bata taɓa Shi ba, zamantakewa ce ta Jahiliyya a wajen ɗabi’un ta, sai dai Manzon Allah bai tāsirantu da waɗannan ɗabi’u dake kewaye dashi na munanan ɗabi’u da kuma ɗabi’u na ƙasƙanci.
 
1⃣ Annabi SAW Yana wulaƙantar da waɗannan gumaka, wanda mutanen shi ke bauta mawa, kuma Ya gano cewa basa amfanar wa basa cutarwa, wataran Annabi SAW Ya kasance tare da bararren bawan Shi Zaidu ɗan Harithah, sai ya zama akwai wani Gunki na Aluminum ana ce dashi ISAF kuma ana ce dashi NA’ILAH, gunki yana tsaye ne a jikin Ka’abah kafirai suna kewaye Ka’abah kuma suna shafar shi, da Manzon Allah yazo sai yayi Dawafi, Zaidu yace: (Nima nayi Dawafi tare dashi, yayin da nazo wucewa, sai na shafi gunkin, sai Manzon Allah Yace: kar ka shafe shi. Zaidu yace: a cikin raina sai nace: Ni ko wallahi sai na shafa, inga me zai faru ne in na shafan, Ni kuwa sai na shafe shi din, sai Manzon Allah Yace: ce nake na hanaka ɗazu! Sai shi Zaidu yace: na rantse da Allah da Ya Girmama Manzon Allah, na rantse da Allah da ya saukar wa da Manzon Allah Littafi, bai taɓa shafar gunki ba, har sanda Allah Ya Girmama shi da Wahayi kuma ya saukar mishi da Littafi). [Dala’ilun Nubuwwah na Al-Imamul Baihaqi].
 
2⃣ Tun da Manzon Allah SAW Yake bai taɓa shan giya ba da ɗai, bai taɓa kusantar Zina ba ko kaɗan, bai taɓa zama wurin Caca ba, ko kuma wurin wata Hōlewa ta wasa na Shashanci ba. Tare da cewa Annabi yana cuɗani da Mutanen shi, yana rayuwa tare dasu, yana tarayya dasu a sauran al’amurran su na al’ada wadanda suka halatta.
 
3⃣ Aliyu Ibn Abi Dalib ya ce: Naji Manzon Allah SAW na cewa tunda nake ban taɓa yunƙurin inyi wani abu daga cikin abubuwan da Jahiliyya suke yi ba, na Waƙoƙi sai dai wasu dareraki guda biyu, na himmatu inje wurin wani Biki, duka sai Allah Ya tsare Ni.  
Manzon Allah Yace: Na rantse da Allah ban sake yunƙuri ba, ban sake komawa ba, duk wani abu da ya shafi irin wannan ban sake koma mishi ba, har Allah Ya Girmama Ni ya mai dani Ni daya daga cikin Annabawan Shi ne. [Dala’ilun Nubuwwah na Al-Imamul Baihaqi]. 
 
4⃣ Jubairu ɗan Muɗh’im yace: wani Raƙumi nawa ya ɓace a ranar Arafah, sai na fita ina neman wannan Raƙumi. Sai naga Annabi tsaye tare da sauran mutanen duniya a Arafah, sai nace: kaga wannan yana daga cikin danginmu masu ra’ayin baza su fita daga harami ba, ya akayi shi kuma yazo nan? 
Abunda yasa Jubairu ya fadi haka, Kuraishawa a ranar Arafah suna tsayawa ne a Muzdalifah basa shigowa Arafah din, basa fita wajen Harami zuwa Arafah, wai sunayin haka ne don su bambance kansu daga sauran mutane, sai Allah Ya datar da Annabi SAW zuwa ga abinda yake daidai tun kafin Allah Ya aiko shi.
 
5⃣ Manzon Allah Ya kasance sananne ne da gaskiya, ba’a taɓa yiwa Annabi shaidar ƙarya ba ko sau ɗaya, abinda ke ƙarfafar wannan; lokacin da Annabi Ya hau dutsen Jabalu Abu Qubais (Safaa), ya kira Mutanen shi, a wurin taro na gari gaba-ɗaya suka mishi irin wannan babbar shaidar sukace: bamu taɓa tuhumar Ka da ƙarya ba, tun kana Ƙarami an sanka da Gaskiya.

✍ *ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)