TUMATIR 2


🌼 *JIKIN DAN ADAM* 0️⃣6️⃣1️⃣🌼

🍅 *_TUMATIR_* 2️⃣🍅

_Fatar Tumatir da 'ya'yan cikinsa sun qunshi sinadarin da yake taimaka wa hanji, Antacid din kuma zai kyautata aikin niqe abinci yadda zai agaza wajen zuqo mafificin Nutrients, Tumatir in aka lura ya qunshi Vitamins B, Vitamin C, Iron, Potassium, Calcium da Magnesium, ga shi yana da mahimmanci wajen zama rigakafin wasu cututtuka, bincike ya nuna cewa, mutanen da suke da Lycopene mai dama a jikinsu hatsarin daskarewar qwaqwalwa ba ta da yawa, wata da ake kira Daniella ta ce gaskiya bincike ya tabbatar da cewa Tumatir bai hana Cancer din qwaqwalwa amma zai iya magance kumburinta._

_Duk da cewa launin Tumatir wani daban ne da wani, sai dai suna da sinadarin Lycopene gaba dayansu, wanda yake maganin tattarar fuska, Tumatir yakan fitar da Antioxidant wato Lycopene don kare fata, ko hana tattarar fatar, duk da cewa ba mai wani babban tasiri ba ne 0amma dai yakan yi, ta ce cin Tumatir din da yawa ba ya nufin zai magance matsalolin gaba daya, sai dai ta yi nunin cewa Tumatir din yana dauke da sinadarin Tyramine da Serotonin da dan dama wanda yakan taimaka wajen canza wa mutun yanayi, har ya ji duniyar ta yi masa daidai._ 

_Tumatir ya qunshi Vitamins ne kawai da Minerals, Fibres, Protein da Carbohydrates, amma bai da Sodium, da Saturated fats da Cholesterol, yana da Vitamin A mai kyau, Thiamine, Niacin, Vitamin B6, Folic acid, Magnesium, Phosphor da Copper, kuma yakan samar da Nutrients mai kyau, Vitamin A, C, K, Potassium da Manganese, daga cikin fa'idojin Tumatir akwai kawar da Germs, wadan da suke haifar da cututtukan jikin dan adam, Tumatir kan motsa nashadin qoda, yakan yi aiki a matsayin mai wanke hanji, kamar yadda yake kau da wahalar niqe abinci, ko fitar da shi bayan ya gama amfani. Tumatir yana da Iron, in kana fama da cutar fatarar jini, to juice din Tumatir, cinsa danye zai taimaka ba kadan ba, za a iya maganin ko sauqaqa , haka zai taimaka wajen magance toshewar numfashi, sinadarin cikin tumbi da yake taimakawa wajen niqe abinci in ya yi yawa, sauran cututtuka na qirji ma Tumatir kan taimaka matuqa, yana ma da amfani ga masu cutar sukari, sabo da Carbohydrates din dake ciki bai da wani yawa, akan yi aiki da shi wajen rage qiba, in ba a yi aiki da shi yadda ya kamata ba kishiyar hakan za ta bayyana, amma Tumatir ya qunshi abubuwa da dama kuma masu amfani._

_Tumatir yakan magance kumburin gabobi, ta wajen hada shi da mai, a dan sanya shi a wuta a ba shi tsoro sai a shafa a inda yake da matsalar don sauqaqa radadin._

Muhadu a rubutu na gaba in shaa Allah

📒 *Abu manar Alqasim*
✍🏻 *Ibnmangaa*
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
Post a Comment (0)