DA ME ZA MU FUSKANCI RAMADAN? 02


*DA ME ZAMU FUSKANCI RAMADAN??*
*002*

 *FALALAR WATAN RAMADAN* 🌕
Yana daga cikin abunda ke sa mutun yayi shiri kan zuwan wani abu idan yasan darajar wannan abun da falalarsa.
Ba shakka kuwa watan Ramadan yana da falaloli da dama wadanda ba za su qirgu ba acikin ayoyin Al-Qurani da Hadisan Manzon Allah (SAW), kadan daga cikin falolinsa akwai:
1. ANA BUDE KOFOFIN ALJANNA A KULLE KOFOFIN WUTA A KUMA DAURE SHEDANU,Ba wani wata daga cikin watanni da ake kulle kofofin wuta a bude kofofin Aljanna a kuma kulle shedanu sai wannan wata mai daraja da falala kamar yadda yazo acikin Sahihaini daga Abu Huraira (RA) Yace:
Manzon Allah (SAW) Yace idan Ramadan yazo ana bude kofofin Aljanna,
a kulle kofofin wuta a kuma daure shedanu” (Bukhari 1898, Muslim 1079)
"إذا جاء رمضان فتحت أبواب الجنة , وغلقت أبواب النار , و ُصِّفدت الشياطين”
2. SABABI NE NA KANKARE ZUNUBBAI
Daga cikin falalar wannan wata na Ramadan ana kankarewa bawa
zunubbai kamar yadda yazo acikin hadisi.
"الصلوات الخمس , والجمعة إلى الجمعة , ورمضان إلى رمضان , مكفرات ما بينهن إذا
اجتنبت الكبائر"
Manzon Allah (SAW) Yace: “Salloli guda biyar, da Jumu‟a zuwa Jumu‟a, da
Ramadan zuwa Ramadan, masu kankarewa ne idan aka nisanci kaba‟irori
(Manyan Laifuka)” (Sahihi Muslim 233)
3. ACIKINSA NE AKE SAMUN LAILATUL QADR
Acikin wannan wata ne ake samun wani dare guda tilo mai daraja wanda
wannan daren yafi dare guda dubu wanda bashi ba, kamar yadda Allah
(SWT) Yace: "إذا جاء رمضان فتحت أبواب الجنة , وغلقت أبواب النار , و ُصِّفدت الشياطين
Don haka wannan daren kadai ya ishi Watan Ramadan darajja da fifiko.
4. AZUMTARSA DA TSAYUWARSA SABABI NE SHAFE ZUNUBBAN DA SUKA GABATA
Hadisi ya tabbata acikin Sahihul Bukhari (2014) da Muslim (760) Manzon Allah (SAW) Yace “Duk wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da neman Lada za‟a kankare masa zunubbansa da suka gabata"
"من صام رمضان إيمانا واحتسابا غفر له ما تقدم من ذنبه"
Haka ma hadisi ya sake tabbata acikin Sahihul Bukhari (2008) da Muslim
(174) Annabi (SAW) Yace: “Duk wanda yayi tsayuwarsa (Ramadan) yana
mai imani da neman lada za‟a shafe masa zunubbansa da suka gabata”.
"من قامه إيمانا واحتسابا غفر له ما تقدم من ذنبه"
5. ACIKINSA NE AKA SAUKAR DA ALQURANI
Daga cikin darajojinsa shine an saukar da Alqurani acikin wannan watan
na Ramadan kamar yadda Allah (SWT) ya bayyana a gurare da dama
acikin littafinSa Mai Tsarki
(شَهۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِیۤ أُنزِلَ فِیهِ ٱلۡقُرۡءَانُ هُدࣰى لِّلنَّاسِ وَبَیِّنَـٰتࣲ مِّنَ ٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡفُرۡقَانِۚ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهۡرَ فَلۡیَصُمۡهُۖ وَمَن كَانَ مَرِیضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرࣲ فَعِدَّةࣱ مِّنۡ أَیَّامٍ أُخَرَۗ یُرِیدُ ٱللَّهُ بِكُمُ ٱلۡیُسۡرَ وَلَا یُرِیدُ بِكُمُ ٱلۡعُسۡرَ وَلِتُكۡمِلُوا۟ ٱلۡعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا۟ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمۡ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ)
[Surat Al-Baqarah 185]
(بِّسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَـٰنِ ٱلرَّحِیمِ إِنَّاۤ أَنزَلۡنَـٰهُ فِی لَیۡلَةِ ٱلۡقَدۡرِ)
[Surat Al-Qadr 1]
Wadannan kadan kenan daga cikin falalolin wannan Wata mai alfarma, wadanda wadannan kadai sun isheshi darajja.
Bisa ga abinda ya gabata na falaloli da darajoji da fifiko da wannan wata mai albarka yake dashi fiye da sauran watanni, ya kamata ace kowane musulmi ya yi tattali domin riskuwar wannan wata kamar yadda Magabata suka kasance suna yi.
*Mu haɗu a Rubutu na gaba*
Post a Comment (0)