DA ME ZA MU FUSKANCI RAMADAN? 05


*DA ME ZAMU FUSKANCI RAMADAN*
*005*
Cigaba..

👉🏻KARATUN QURANI
Magabata na qwarai sun kasance sukan zare damtse wajen karatun AlQur‟ani tun kafin zuwan Ramadan.
Anas bin Malik (RA) Yace: “Musulmai sun kasance idan watan Sha’aban ya shigo za su dage wajen karatun Al-Qurani, za su fitar da Zakkar dukiyoyinsu domin karfafawa Miskinai da masu rauni akan azumin watan Ramadan”Salama bin Kuhail(Rahimahullah) Yace: “Ya kasance ana cewa watan Sha‟aban watan makaran ta (Al-Qur‟ani) ne” Amru bin Qais (Rahimahullah) Ya kasance idan watan Sha‟aban ya shigo zai kulle shagonsa ya shagaltu da karatun Al-Qurani.
Abubakr Al-Balkhi (Rahimahullah) Yace: “Watan Rajab watan shuka ne,watan Sha‟aban watan ban ruwa ne, watan kuma Ramadan watan Girbi ne” Ya kara da cewa: “Misalin watan Rajab kamar Iska ne, Misalin watan Sha‟aban kamar Girgije ne, Misalin kuma watan Ramadan kamar Ruwan Sama ne. 
Duk wanda bai yi shuka ba acikin Rajab, bai yi ban ruwa ba acikin Sha‟aban toh ta ya ya zai yi girbi acikin Ramadan ? (Lada’iful Ma’arif shafi 141
*Mu haɗu a Rubutu na gaba da ikon Allah*
✍🏻MUSA YAQOUB SULAIMAN (IBNKHASIR)
Post a Comment (0)