_*👩🍳A A KICHEN FOOD/SANKS👩🍳*_
*DAY-I*
_Shinkafa da miyar albasa,sai hadin salad da /meat-pie/da/Shayin na'a na'a/da dabino._
*🧅🧅MIYAR ALBASA🧅🧅*
_Kayan hadi_
_Albasa🧅_
_Attaruhu🌶️_
_Tumatur🍅_
_Kayan ƙamshi🌰_
_Nama/Kaza🥩🍗_
_Maggi/Gishiri🧂_
_Curry🍧_
_Mai🍾_
*YADDA AKE YI*
_Dafarko zaki fara gyara nama ki, ki tafasa shi da kayan ƙamshi da ɗanɗano sai ki yankashi ƙanana in kuma manyan kike so zaki iya barinsa sai ki soyashi sama-sama ki ajiye shi a gefe,ki ɗauki albasa dayawa yadda zata ji ki kintata yawan miyar taki sai ki gyara ta ki yankata siri-siri yankan faɗi ki ajiye ta a gefe._
_Sai ki gyara kayan miyar taki ki wanke ki samu wuƙa ki yanka tumatur ɗinki ƙanana-ƙanana shi kuma attaruhun ki jajjagashi sai ki ɗauko tukunyar miyar ki ki ɗora a kan wuta by minti ta ɗauki zafi ki fara zuba mai aciki ki danƙi ƴar albasa ita ma ki zuba ya soyo sama-sama sai ki ɗauko yankaken tumatur ɗin nan da kika yanka ki zuba akan mana ki juyasu sosai by minit ki zuba attaruhun shima akai ki juya su haɗa jikinsu idan kin juya sai ki ɗauko wannan naman naki dakika soya sama sama shima ki zuba a kai ki juya ya ɗan soyu sai ki zuba magi da gishiri da kayan ƙamshi da curry ki,idan kin zuba sai ki juya ki ɗan ji tis ɗin ki ɗauko me gayya me aikin wato Hajiya Albasa ki zuba ta akai ki juya ko ina ya game jikinsa by 5minit ko 6ki sauke sai aci da wannan farar shinkafar😋_
_*👩🍳🫑A A KICHEN FOOD/SANKS🫑👩🍳 07065014495*_