*HUKUNCIN DUKAR MACE A ADDININ MUSULUNCI?*
https://chat.whatsapp.com/LRPQDrs7qSoKXuSspoPkFm
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum, mene ne hukuncin namiji mai duka, har ya sumar da matarsa, wani lokaci har ya yi mata targade, shin ya halasta a zauna da irin wadannan mazan, domin dukan mace shi ke sanya wasu matan su nemi hanyar kare kansu, idan da tsautsayi har a rasa rai. Nagode.
*AMSA*👇
Wa'alaikumus Salamu, duk lokacin da mace ta saɓa wa mijinta a harkar zamantakewar aure, to Shari'a ta ba da bayanin matakai da ya kamata a bi don ganin an yi wa mata gyara, idan muka koma Alqur'ani mai girma za mu ga inda Allah Maɗaukakin Sarki ke cewa:
"Matayen da kuke tsoron saɓawarsu, to ku yi masu wa'azi, ku qaurace masu a shimfiɗa, ku dake su, amma idan suka yi maku biyayya kada ku nemi hanyar cutar da su, lallai Allah Ya kasance Mai ɗaukaka ne Mai girma. Suratun Nisá'i aya ta 34.
Malaman Tafsiri sun nuna cewa waɗannan matakai guda uku su ne miji zai bi wurin mu'amala da matarsa a lokacin da ta saɓa wa umurninsa ko umurnin Allah, wato da farko zai fara yi mata wa'azi da nasihohi ne, ba sau ɗaya ba, a lokuta mabambanta, idan ba ta gyara ba sai ya qaurace mata a shimfiɗa, wato ya daina kwanciya da ita, idan duk ta qi gyara halinta bayan waɗannan matakai guda biyu, to yana iya dukanta amma ba duka mai cutarwa ba, kamar yadda malamai suka bayyana a Tafsirai. Amma wasu malaman sun ce barin dukan ya fi, duk da kasancewar addini ya ba da damar a yi.
To a nan ne ake samun wasu mazajen da ba su san abin da suke yi ba, idan suka zo dukan matayen nasu sai su yi masu dukan mahaukata, har a ji ma wata rauni, to ba haka ayar take nufi ba, irin dukan da ake nufi shi ne duka ba mai cutarwa ba, duka ba mai cutarwa ba kuwa shi ne dukan da idan aka yi shi ba zai nuna alamar duka ba, kamar yadda malamai suka bayyana, kuma barin dukan ya fi alheri, amma fa ya halasta a Musulunci bayan an bi matakin nasiha da qauracewa shimfiɗa duk abu ya qi gyaruwa kamar yadda ayar Alqur'ani ta nuna.
Saboda haka ba dai-dai ba ne a bayar da aure ga wanda aka san yana sumar da matarsa ba, ko wanda yake dukan matarsa har sai ta yi targaɗe ko makamancin haka ba, saboda duka ba mai cutarwa ba aka ce, idan kuma ita mace ta ga za ta iya zama da irin wannan miji ganin damarta ne ba za mu hana ta ba.
Kuma lallai mata ya kamata su ma su sani lallai maganar dukan nan addini ya aminta da shi amma fa ba mai cutarwa ba, saboda haka, masu kore dukan kwata-kwata su ce Musulunci bai zo da shi ba kuskure ne, sai dai barin dukan ya fi alheri.
Domin neman qarin bayani a duba TAFSIRUR RAÁZIY, wato MAFAÁTEEHUL GAIB a qarqashin aya ta 34 na SURATUN NISÁ'I.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*