YA RABON KWANA ZAI KASANCE A LOKACIN LOCKDOWN
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
*TAMBAYA*❓
Malam Allah ya Kara Daukaka.
To Malam Ya Matsayin wannan Lockdown Da aka Sa Mazajenmu a gida.
Zakaga Miji yana da Gida Biyu Alahlin kuma Gida biyun nan ba a Kusa suke da Unguwanni ba. Ma'ana Zakaga Akwai Tazara Tsakanin Unguwar Matarsa Uwar gidan da kuma Amaryar sa. Wanda Kafin a fito waje za a Kai akalla Sati Guda.
To Malam Yaya Ragon kwana yake. Wanda a baya da yana Kwana Biyu, Amma yanzu wannan dokar ta Rashin na tsawon Sati ta Ritsa shi a Gidan Amarya? Wanda ba zai yayi ba sai yayi sati Guda a Chan.?
*AMSA*👇
Mafi Alkairin koyi shine koyi da Fiyayyen Halitta Saw.
Wata Mas'ala Mai Kama da wannan ta Taba Faruwa a Gidan Manzon Allah saw. A Daidai Lokacin da Ya Auri UMMU SALAMA, tana Amarya. Manzon Allah saw ya yi Mata Kwananta Ukku da Ake Baiwa Bazawara idan an Aureta a Matsayin Amarya. Kafin nan kuma Sai Ayi Rabon Kwana Kamar Yadda Hadisin Anas ya Nuna.
Sai Da Manzon Allah Saw Zai Fito daga Dakinta Domin Tafiya daya dakin na Gaba. Na wadda Take da Hakkin Kwana, Sai Ummu Salama ta Rike shi, Tace Ba Inda Zashi. Sai dai yaci gaba da Kwana a dakinta.
Sai Manzon Allah saw Yace. IDAN KIN SO ZANYI MIKI KWANA BAKWAI. AMMA IDAN NAYI MIKI KWANA BAKWAI, TO FA SAURAN MATA NA ZANYI MUSU KWANA BAKWAI KAMAR YADDA KE MA NAYI MIKI KWANA BAKWAI. Da Taga Lalle za a dade Kafin a dawo Dakinta. Sai Tace Bata Yarda ba. Sai manzon Allah saw ya Tafi dakin Gaba, na Wadda take da kwana.
Sabida haka Anan, Zamu Dauki Hukuncin da Manzon Allah saw ya yi, Inda Yace da Ummu Salama, IDAN NAYI MIKI KWANA BAKWAI, TO FA WAJIBI NE ZAN YIWA SAURAN MATA NA KWANA BAKWAI.
Sabida haka Anan. Matar da Ta Rasa miji, Za'a Rama Mata Kwanakin da Ba ayi Mata ba. Ma'ana Zai Rama Mata Adadin Kwanakin da ya yiwa Waccan Matar da Wannan Abin y Rutsa a gidanta. Wannan shine Zaifi Zama Adalci.
Amma idan sun Fuskanci Abin ta Fuskar Larura kuma Aka Lallaba ta Ta yafe, shikenan Magana ta Wuce.
Allah ya Kawo Mana Aminci a wannan Kasa Tamu da kuma Sauran Kasashe na Musulmai Gabaki daya.👏
Allah ya Kare Mu daga wannan Cuta da ta Addabi Duniya Gabaki daya.👏
Allah Shine Masani.
Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*